fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Casemiro yace a koda yaushe tunanin su shine su taimaka wajen yaki da cutar Coronavirus/covid

Casemiro yayi jawabi ga wasu matasan dake son wasan kwallon kafa a wani taro da suka hada a yanar gizo na kiyaye yara da kuma wayar masu da kai gami da cutar coronavirus data sa aka dakatar da gasar wasannin duniya baki daya.

 

Casemiro yace abubuwa suna matukar wahala a halin yanzu amma ya kamata mu cigaba da aikin mu, kuma aikin shine mubi umarnin gwamnati mu cigaba da zama a gida kuma mu taimaka iya bakin kokarin mu. Kuma yayi tambayoyi gami da wasannin Real a gasar champions lig da la liga.
Ya Kara da cewa tabbas suna so su ci gasar champions lig da kuma la liga amma yanzu ba shine a tunanin suba, tunanin su shine su taimaka wajen yaki da annobar cutar coronavirus.
Dan wasan Brazil din yace a koda yaushe yanada jagora,Kuma jagoran shine zidane wanda ya kasance kochin kungiyar Real Madrid. Yana son zidane sosai saboda yana yabon yan wasan shi kuma yana son su gaba daya baya fada da kowa.
Dan wasan yace yana daukar sauran abokan aikin shi kamar iyalin shi na biyu kuma gaba dayansu abokai ne. Babban burin su shine samun nasara a koda yaushe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Labari da Dumi Duminsa: Chelsea ta shirya daukar tauraron dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo

Leave a Reply

Your email address will not be published.