
Bayan Sallah za mu yi aure>>Saurayin Baturiya na Panshekara
Saurayin nan da budurwarsa ‘yar Amurka ta biyo shi Kano mai suna Isa Suleiman Panshekara ya ce a bayan Karamar Sallah zai angwance da amaryarsa Janine Sanchez.
Saurayin mai shekara 26 ya ce sun dage shagulgulan bikin nasu ne saboda wasu dalilai ba kamar yadda ake rade-radi ba a shafukan sada zumunta cewa saboda Shugaba Trump ya hana ’yan Najeriya shiga Amurka ne.
“Sosai kuwa, yanzun nan kafin ka kira ni muka gama waya ta bidiyo, ka ga kuwa alama ce da ke nuna muna tare ba kamar yadda kafafen watsa labarai ke fada ba.”
Ya ci gaba da cewa: “Babu wani bambanci gaskiya, illa in ce ma so ne ya sake karuwa.
“Mafi yawa ta Facebook Messenger muke magana kuma waya muka fi yi ba rubutu ba (chatting) ba kamar...