
An kama matan da ake zargi da auren junansu a Sokoto
Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato ta kama wadansu mata biyu da ake zargin sun yi auren junansu (auren jinsi) suna zaune tare tsawon wata hudu. Hukumar na kuma zarginsu da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Unguwar Obalande a Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu da ke Jihar Sakkwato.
Kwamandan Hukumar ta Jihar, Dokta Adamu Bello Kasarawa wanda ya jagoranci jami’ansa zuwa kamen, ya shaida wa Aminiya cewa “Wannan lamari da muke ji a wasu wurare ya zo mana nan, mace ta auri jinsinta, duk wanda ya ji haka zai yi mamaki yadda al’umma ke kara lalacewa. Matan sun yi alkawarin ba rabuwa a tsakaninsu ta hanyar sanya zobe da shan jinin juna don kara alakar.”
Ya ce: “Bincikenmu ya gano sun fara alaka da juna ne tun a Jihar Kaduna, kuma akwai wadanda suka sanya su cikin lamarin.”...