Yawan wanda suka mutu bayan harin kunar bakin wake sun kai 30, guda 100 sun jikkata a jihar Borno
Rahotanni daga jihar Borno na cewa, yawan wadanda suka mutu ya karu zuwa 30 daga 8 da jami'n tsaro suka bayyana a jiya.
Hakanan yawan wadanda suka jikkata ya karu zuwa 100.
Rahoton jaridar Vanguard ya ruwaito cewa, sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta ya tabbatar da faruwar lamarin.
Jaridar tace Timta ya bayyana mata cewa 'yar kunar bakin wake ta farko ta je wajan bikine tare da yara inda ta tayar da bam sannan an samu ta biyu itama taje wajan wani bikin ta sake tayarwa.
Timta ya kara da cewa, an sake samun wani tashin bam din a karo na 3.
A baya dai, jaridar Premium times ta ce 'yan kunar bakin wake 4 ne suka tayar da bamabamai a Garin na Gwoza.
Timta dai yace ba'a kammala samun bayanai ba amma zuwa yanzu mutum 100 sun jikkata kuma an garzaya da wasu zuwa Maidu...