fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Breaking News

Sanatoci sunyi watsi da kudurin kafa dokar karba karba da zata baiwa kowace kabila damar shugabanci a Najeriya

Sanatoci sunyi watsi da kudurin kafa dokar karba karba da zata baiwa kowace kabila damar shugabanci a Najeriya

Breaking News, Siyasa
Majalissar dattawa tayi watsi da kudurin kafa dokar karba karba wadda zata baiwa kowace kabila damar mulkar Najeriya. Sanatan dake wakiltar kudancin jihar Benue, Abba Moro ne ya nemi a kafa wannan dokar, amma sai dai burin nasa bai cika ba domin abokan aikin nasa sun juyawa shawarar tashi baya. Inda wasu daga cikinsu suka bayyana cewa kudin tsarin mulki ya baiwa kowa damar tsayawa takarar neman shugabanci saboda haka ba sai an kafa dokar ba. Inda wasu suka bayyana cewa tsohon shugaban kasa GoodLuck Ebele Jonathan yayi mulki ba tare da an kafa wannan dokar ba.
‘Yan Boko Haram sama da 90,000 sun mika wuya a shekara guda, cewar Zulum

‘Yan Boko Haram sama da 90,000 sun mika wuya a shekara guda, cewar Zulum

Breaking News, Tsaro
Gwamnan jihar Maiduguri, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa 'yan ta'addan ISWAP dana Boko Haram sama da 90,000 sun mika wuya a shekara guda. Gwamnan ya bayyana hakan ne a taron majalissar dinkin duniya karo na 77 da suka gudanar a birnin New York dake kasar Amurka. Inda yace a fadin duniya ba a taba samum irin wannan tarihin ba da dumbin 'yan bindiga suka tuba a shekara guda ba, saboda haka matsalar tsaro tazo karshe. Gwamnan ya jinjinwa shugaba Buhari kan namijin kokarin daya keyi wurin magance matsalar tsaron, inda yace kafin zuwan Buhari Boko Haram ce ke mulkin jihar amma yanzu an wayi gari ko karamar hukumar guda basa juyawa.
Zaben 2023 zai sha banban dana 2019, cewar hukumar zabe

Zaben 2023 zai sha banban dana 2019, cewar hukumar zabe

Breaking News, Siyasa
Hukumar zabe ta kasa, wato INEC ta bayyana cewa zabe mai zuwa na 2023 zai sha banban dana 2019 sosai domin sun shirya masa. Kwamishinr dake lura da tsare-tsaren gudanar da zaben ce ta bayyana hakan, Farfesa Rhoda Gumus a wani astisayi da suka gudanarwa a jihar Gombe na kwanaki biyu. Inda tace zaben 2023 zabe ne wanda kowa zai kada kuri'arsa ba fargaba kuma zabin talaka ne zai hau mulki babu magudi. Tace zaben jihar Ekiti da Osun misali ne na cewa sun shiryawa zaben shugaban kasa na 2023 kuma babu wanda zai yi magudi.
Ya kamata mubi doka muyi gwajin shan kwaya, dan takarar gwamna a jihar Katsina ya fadawa abokan adawarsa

Ya kamata mubi doka muyi gwajin shan kwaya, dan takarar gwamna a jihar Katsina ya fadawa abokan adawarsa

Breaking News, Siyasa
Dan takarar gwamna a jihar Katisina karkashin tutar PRP, Imran Jafar Jino ya bayyana cewa ya kamata duk abokan adawarsa suyi gwajin kwaya kamar yadda doka ta tanadar. Ya bayyana hakan ne bayan shi yayi nashi gwajin kuma ya gabadatr dashi ga manema labarai, inda yace hukumar NDLEA da kuma babban asibitin Kastina ne suka yi masa gwajin. Inda sakamakon gwajin ya nuna cewa baya shan kwaya, saboda haka ne yace ya kamata suma sauran subi wannan dokar ta hukumar NDLEA, saboda bai kamata dan kwaya ya mulki jama'a ba. A karshe yasha alwashin habbaka tattalin arzikin jihar ta Katsina da kuma kawo cigaba da zaman lafiya mai dorew idan har suka zabe shi yayi nasara a zabe mai zuwa.
‘Yan bindiga sun kai hari masallacin juma’a sun kashe masallata 15 a jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun kai hari masallacin juma’a sun kashe masallata 15 a jihar Zamfara

Breaking News, Tsaro
'Yan bindiga sun kai hari madallacin juma'a a jihar Zamfara sun kashe masallata guda 15 a karamar hukumar Bukuyyum. Lamarin ya faru ne a kauyen Ruwan Jere a ranar juma'ar data gabata kamar yadda al'ummar yankin suka bayyana, inda suka ce 'yan bindigar sun boye bindugun nasu ne a jikinsu. Kafin daga bisani suka budewa masallatan wuta suka kashe guda 15 suka raunata wasu da dama yayin da kuma wasu suka bata ba a gansu ba. Wannan lamarin ya faru ne makonni uku bayan 'yan bindigar sun kai hari masallacin juma'a a kauyen Zugu duk dai a karamar hukumar ta Bukuyyum.  
A shirye nake na tayar maku da hanakali idan hakan kuke so, Bello Turji ya fadawa gwamnatin tarayya

A shirye nake na tayar maku da hanakali idan hakan kuke so, Bello Turji ya fadawa gwamnatin tarayya

Breaking News, Tsaro
Kasurgumin dan ta'addan arewacin Najeriya, Muhammadu Bello Turji wanda aka fi sani da Bello Turji ya bayyana bacin ransa akan harin da dakarun sojin sama suka kai masa. Dakarun sojin sama sun kai masa wani mummunan hari ne a makon daya gabata inda har suka kashe masa iyalansa da kuma mayakansa sosai a wani taton biki da suka halatta a karamar hukumar shinkafi dake Zamfara. Inda yace ya tuba tuni kuma gwamnatin ta bayyana jin dadinta akan hakan amma yanzu taci amarsa, kuma tsawon watanni biyar kenan bai sace kowa ba kuma bai kaiwa kowa hari ba. Amma idan gwamnatin tana son ya cigaba da sace al'umma da kuma kai hare hare to shima a shirye yake, domin harin da suka kai masa har ya shafi al'ummar da babu ruwansu da ta'addanci.
Gwamnatin tarayya ta cewa ASUU tabi umurnin kotu na komawa makaranta kafin su cigaba da sasantawa

Gwamnatin tarayya ta cewa ASUU tabi umurnin kotu na komawa makaranta kafin su cigaba da sasantawa

Breaking News, Ilimi
Gwamnatin tarayya ta cewa kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU ta koma kan aiki kamar yadda kotu ta bata umurni a shari'ar da suka gudanar ranar laraba. Ministan kwadago Sanata Chris Ngige ne ya bayyana hakan, inda yace masu su fara bin umurnin da aka basu kafin su cigaba da sasantawa da gwamnatin tarayyar kan bukatunsu. Kungiyar Malaman ta kasance tana yajin aiki har na tsawon watanni bakwai kan gwamnatin tarayya bata biya mata bukatunta ba. Amma gwamnatin tarayyar ta maka ta a kotu inda har aka bata umurnin komawa kan aiki cikin gaggawa amma ASUU ta daukaka wannan karan domin bata gamsu dashi ba.
Kuji da taku matsalar ku rabu da PDP, Atiku ya fadawa APC

Kuji da taku matsalar ku rabu da PDP, Atiku ya fadawa APC

Breaking News, Siyasa
Dan takarar shugabam kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyanawa jam'iyyar APC cewa taji da tata matsalar ta rabu da PDP. Atiku ya bayyana hakan ne bayan APC tace ya fadi zaben shugaban kasa warwas saboda rikicin gida da suke fama dashi. Wanda hakan yasa hadimin Atiku ya yiwa APC raddi cewa babu ruwanta da rikicinsu itama taji da matsalar data shafeta ba wai ta wasu ba. A yau ranar juma'a ne APC tace Atiku zai sake fadi zaben shugaban kasa kamar yadda yayi a baya domin Nyesom Wike ya sasu a gaba.
PDP ta fadi zaben shugaban kasa warwas saboda rikicin gida, cewar APC

PDP ta fadi zaben shugaban kasa warwas saboda rikicin gida, cewar APC

Breaking News, Siyasa
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa dan takatar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya fadi zaben shugaban kasa na shekarar 2023 warwas. Mai magana da yawun kungiyar dake yiwa APC yakin neman zaben ne ya bayyana hakan a yau ranar juma'a wato Mr Bayo Onanuga. Inda yace rikicin gida na jam'iyyar PDP ne yasa Atiku Abubakar zai sake fadi zaben shugaban kasar Najeriya kamar yayi a baya. A karshe yace gwamnan PDP na jihar Rivers, Nyesom Wike ne sanadiyyar rikicin gidan nasu wanda yaketa fafutuka kan tsige shugabansu Iyorchia Ayu.
Matasan PDP sun zargi Wike da yiwa Atiku zagon kasa, inda suka ce yanawa Tinubu kamfe

Matasan PDP sun zargi Wike da yiwa Atiku zagon kasa, inda suka ce yanawa Tinubu kamfe

Breaking News, Siyasa
Kungiyar matasan jam'iyyar PDP ta bayyana cewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike na yiwa dan takarar shugaban kasarsu zagon kasa, Wato Atiku Abubakar inda suka ce yana yiwa dan takarar jam'iyyar adawarsu ta APC yakin neman zabe, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu. Shugaban kungiyar matasan Ibrahim Bala Aboki ne ya bayyana hakan, inda yace Wike ya kulla wata yarjeje iya ne da tsohon gwamnan jihar Legas din. Kuma yace zanga zangar da Wike yakeyi ta cewa dole a tsige shugaban jam'iyyar itama wani salo ne na jawo hankalin jam'iyyar yake yi da kuma dan takararta don ya bata masu lokaci.