
“Ba zamu bari a gudanar da zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa ba indan har ASUU basu janye yajin aiki ba”>>kungiyar daliban Najeriya, NANS
Kungiyar daliban Najeriya, NANS ta bayyana cewa ba zata bar wata jam'iyya ta gudanar da zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa ba a jihar Abuja idan ba'a bude masu makarantu ba.
Shugaban kungiyar, Sunday Asefon ne ya bayyanawa Vanguard hakan, inda yace yanzu watanni uku kenan da kulle makarantu amma ba wani mataki da aka dauka.
Saboda haka suna kira ga gwamnati dama ASUU bakidaya su sasanta kansu idan ba haka to ba zasu bari a gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa ba a jihar Abuja.