Wasu malamai sun ce Jefe me aure Mazinaci bashi da asali a Musulunci>>Inji Sheikh Ibrahim Maqari
Farfesa, Ibrahim Maqari ya bayyana cewa akwai malamai da suka tafi akan cewa, Jefe me aure da yayi zyna bashi da Asali a Musulunci.
Ya bayyana hakane inda yace asali wasu yahudawa ne suka je wajan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)neman fatawa akan Mazynaci me aure saboda dokar a addininsu tana da tsauri.
Yace Amma sai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yaje a dauko littafinsu a musu hukunci da abinda littafinsu yace.
https://www.tiktok.com/@dahimmarshehu0/video/7694287087213890824?_r=1&_t=ZS-9APqbyoPyrf







