Kwankwaso Ya Bada Gudunmawar Naira Milyan Hamsin Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Borno
Daga Abubakar Shehu Dokoki
Ɗan Takarar Shugaban ƙasa, ƙarkashin Tutar Jam'iyyar NNPP a zaɓen daya gabata na 2023 Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bada wannan tallafin ne a wata ziyara ta musamman da ya kai jihar Borno domin jajanta musu bisa ambaliyar ruwan da ta yi sanadiyyar raba ɗaruruwan mutane da gidajensu.
Kwankwaso ya miƙa wannan tallafi ne ta hannun Gwamnatin Jihar Borno.