fbpx
Wednesday, March 29
Shadow

Gist/Social Media

Yakamata a soke duk wani hutu da ake baiwa ma’aikata a Najeriya – Surukin Dangote, Jamil Abubakar

Yakamata a soke duk wani hutu da ake baiwa ma’aikata a Najeriya – Surukin Dangote, Jamil Abubakar

Gist/Social Media
Kaftin Jamil, surukin hamshakin attajirin Afrika Aliko Dangote ya ce ya kamata a soke duk wani hutun bukukuwan da ake yi a Najeriya. Jamil wanda dan tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mohammed Dikko Abubakar ne, a cikin sakonsa na Twitter, ya bayyana cewa an bar Najeriya a baya sosai, dan haka akwai bukatar mu dage damtse domin a kai gaci. Ya kuma ce hutun kwana daya ya ishi ma'aikata hutu.
Al-ummomin garuruwan Medu, Danmadai da Kanyu sun sauke Al-qur’ani Mai girma domin Allah ya kwato masu hakkinsu akan gwamnatin jihar Jigawa

Al-ummomin garuruwan Medu, Danmadai da Kanyu sun sauke Al-qur’ani Mai girma domin Allah ya kwato masu hakkinsu akan gwamnatin jihar Jigawa

Gist/Social Media
A yau Asabar 22 ga watan Ramadan wanda yayi daidai da 23 ga watan Afrilu 2022, al-ummomin garuruwan Medu, Danmadai, Kore balatu,Kore babba, gayawar malam, kagadama, Garin chiroma, da fulaninsu sun gabatar da Sallah nafila da saukar Al-qur'ani Mai tsarki domin Allah ya kwato masu hakkinsu akan gonakinsu da gwamnatin jihar Jigawa ta karbe masu. Idan ba ku manta ba a ranar 3 ga watan Afrilu mun kawo maku labarin mutanen wadannan yankin da suka gabatar da Al-qunut kan gonakinsu da suke zargin gwamnatin jihar Jigawa ta hada baki da wani mutumin kasar china Mai suna Mista Lee mai kamfanin GNA (Great Northern Agribusiness Company), wanda shi ne suke zargin ana sayarwa da gonakinsu da aka karbe masu. Al-ummomin sunce ana karbe masu gonaki a basu kudaden da ba su taka kara ba, a zantawa d...
Muddin EFCC ba ta gayyaci jami’in gwamnatin da ya biya miliyan 100 na fam din tsayawa takarar shugaban kasa na APC ba, to suna aiki ne da son zuciya – Reno Omokri

Muddin EFCC ba ta gayyaci jami’in gwamnatin da ya biya miliyan 100 na fam din tsayawa takarar shugaban kasa na APC ba, to suna aiki ne da son zuciya – Reno Omokri

Gist/Social Media
Reno Omokri ya ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, za ta zama mai nuna son kai, idan har ta kasa gayyatar duk wani jami’in gwamnati da ya biya naira miliyan 100 domin samun fom din tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC. Idan dai za a iya tunawa, a ranar Larabar da ta gabata ne jam’iyyar APC ta sanar da cewa an biya fam miliyan 100 na fom din takarar ta na shugaban kasa yayin da na gwamnonin zai kai Naira miliyan 50. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Reno ya bayyana cewa hukumar EFCC ta gayyaci dan kasuwa Obi Cubana domin amsa tambayoyi bayan ta shaida yadda ya kashe miliyoyin kudade domin jana’izar mahaifiyarsa. Reno ya bayyana cewa idan har hukumar ta gaza gayyato duk wani jami’in gwamnati da ya biya Naira miliyan 100 domin ya samu fom din...
Ba zan halarci jana’izar mahaifina mara amfani ba – Jaruma Chioma Toplis

Ba zan halarci jana’izar mahaifina mara amfani ba – Jaruma Chioma Toplis

Gist/Social Media
Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Chioma Toplis, a ranar Litinin din da ta gabata ta girgiza da yawa daga cikin masoyanta da mabiyanta a lokacin da ta bayyana cewa ba za ta taba halartar jana'izar mahaifinta ba idan ya rasu. Chioma mai zafin rai ta bayyana mahaifinta a matsayin malalaci, wawa kuma mayaudari. Ta yi wannan bayanin ne a lokacin da take mayar da martani ga wani sakon Twitter da wani @jayritse ya wallafa. Mutumin ya yi zargin cewa mahaifinsa dattijo ne a coci kuma mai dukan mahaifiyarsa a gida. Da take mayar da martani a shafinsa na Twitter a shafinta na Instagram, jarumar ta ce; "Na dauka mu kadai ne ke da uba marar amfani. Shi ma Dattijo ne a coci kuma mai dukan mahaifiyarmu. Muna cikin jirgi daya, mahaifiyata ma ta bar mahaifina saboda dalilai da ya...
Sama ba za ta fado kasa ba kan karancin man fetur– Femi Adesina

Sama ba za ta fado kasa ba kan karancin man fetur– Femi Adesina

Gist/Social Media
Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya ce ‘yan Najeriya za su fita daga karancin man fetur da suke fama da shi a halin yanzu. Adesina ya ce sama ba za ta fado a kasa ba kan karancin man fetur da ake fama da shi, kuma ‘yan Najeriya za su ci gaba da rayuwa kamar ko da yaushe. Ya bayyana hakan ne a sabon labarinsa na mako-mako a ranar Alhamis mai taken “KNOCK, KNOCK. WHO’S THERE?” Mai taimaka wa shugaban kasar ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun fuskanci irin wannan yanayi a baya kuma sun rayu, dan haka ko a yanzu zasu rayu.
Hotuna/Bidiyon: Wani matashi a Sakkwato ya kirkiri hannun da zai taimakawa mutane masu hannu daya ko kuturta

Hotuna/Bidiyon: Wani matashi a Sakkwato ya kirkiri hannun da zai taimakawa mutane masu hannu daya ko kuturta

Gist/Social Media
Abubakar Muhammad wanda aka fi sani da Abba injiniya, Dan asalin Jihar Sakkwato ne wanda Allah ya baiwa fasahar kirkiri musamman fannin robot (wato abubuwa masu sarrafa kansu). A yanzu haka ya kirkiri wani hannu da yake aiki tamkar hannun mutum domin mutane masu fama da lalura kuturta, ko wadanda suka rasa hannu daya da makamanta su. A fira da nayi da shi a yau da safe, yayi kira da Gwamnatin da kamfanoni da su tallafawa irinsu domin kawo cigaba a cikin wannan kasa ta Nageriya. Kalli bidiyon yadda abun ke aiki;
Man commits suicide because his manhood refused to stand

Man commits suicide because his manhood refused to stand

Gist/Social Media
A 22-year-old NCE graduate, Idris Shuaib, has reportedly committed suicide in Kwara North Senatorial District over his inability to have sex with women. The incident occurred on Thursday in Gwanara community, Baruten Local Government Area of Kwara State. Reports reaching DAILY POST in Ilorin said the entire Ankara Wooro compound in Gwanara community was thrown into a mourning mood when the lifeless body of Idris was discovered dangling on a cashew tree. An uncle of the deceased said “Idris left home very early on Thursday, telling his father that he wanted to go to the farm as his usual routine not knowing he had another fatal motive this time around.” Spokesman of the Kwara State Command of the Nigeria Security and Civil Defence Corps, NSCDC, Babawale Zaid Afolabi, who con...