Sunday, July 21
Shadow

Gyaran Gashi

Gyaran Gashi

Gyaran Gashi, Kwalliya
Akwai hanyoyi da yawa na gyaran gashi wanda ba ma sai kin sayi mai ba idan kinso. A wannan rubutu, zamu kawo muku abubuwan gyara gashi daban-daban wanda za'a iya hadawa a gida: Man Zaitun: Ana samun man zaitun wanda ba'a hadashi da komai ba, a rika amfani dashi wajan gyaran gashi, man zaitun yana taimakawa sosai wajan kara yawan gashi, hanashi karyewa, sa gashi ya rika sheki da sauransu. Idan gashin kanki ya lalace, ko yana yawan bushewa ko yana kaikai, man zaitun na magance wadannan matsaloli. Ana shafa man zaitun akai, bayan mintuna 30 sai a wanke ko kuma idan anzo kwanciya sai a shafashi, da safe a wanke da ruwan dumi. Man Kwakwa: Bayan Man zaitun, ana kuma amfani da Man Kwakwa wanda ba'a gaurashi da komai ba wajan gyaran Gashi. Shima ana shafashi zuwa mintuna 30 sai a w...