fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Ibada

Mutane 21 sun mutu bayan da bam ya tashi a masallacin Kabul

Mutane 21 sun mutu bayan da bam ya tashi a masallacin Kabul

Breaking News, Ibada
Mutane 21 sun mutu yayin da wasu guda 33 suka samu raunika biyo bayan bam din daya tashi a masallacin Kabul ranar laraba. Manema labarai na Aljazeera ne suka ruwaito wannan labarin, inda sukace bam din ya tashi ne yayin da ake yin sallar isha'i. Kuma hatta limamin masallacin ya rasu yayin da su kuma sauran mutanen da suka samu rauni ke jinya a asibitin dake Kabul hadda yaro dan shekara bakwai. Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar wannan lamarin kuma tace suna cigaba da gudanar da bincike akan dalilin daya haddasa wannan harin.  
Allahu Akbar: Daya daga cikin mahajjatan Kano ya rasu anyi masa janaza a Masjidil Haram

Allahu Akbar: Daya daga cikin mahajjatan Kano ya rasu anyi masa janaza a Masjidil Haram

Breaking News, Ibada
Daya daga cikin mahajjatan jihar Kano, Sani Idris Muhammad ya mutu a kasa mai tsarki ranar asabar. Sakataren hukumar dake lura da walwalar Alhazai na jihar ne ya bayyanawa manema labarai hakan, wato Abba Muhammad Danbatta. Inda yace Idris ya mutu ne bayan daya yi wata takaitacciyar rashin lafiya a babban asibitin kasar mai tsarki. Kuma sun yi masa janaza a Masjidil Haram an binnesa bisa koyarwa addinin Musulunci, yayin da kuma suka yiwa iyalansa ta'aziyya.
Daya daga cikin mahajjata mata na jihar Taraba ta bata a kasa mai tsarki

Daya daga cikin mahajjata mata na jihar Taraba ta bata a kasa mai tsarki

Breaking News, Ibada
Daya daga cikin mahajjata mata na jihar Taraba ta bata bayan ta kammala aikin hajji a kasa mai sarki. Mahajjatan da suka dawo gida Najeriya ne suka bayyana hakan a ranar asabar da jirginsu na karshe na jihar ya sauka a Najeriya. Inda suka ce Hassan Abdullahi Bamuze ta bata a kasar mai tsarki bayan sun kammala aikin hajji tare da ita. Hukumar dake lura da jin dadi mahajjata tace zatayi iya bakin kokarinta domin ta ceto ta.
Bazan janye karan dana shigar kan hana matan Musulmai sanya Hijabi ba, cewar lauya Malcolm Omirhobo

Bazan janye karan dana shigar kan hana matan Musulmai sanya Hijabi ba, cewar lauya Malcolm Omirhobo

Breaking News, Ibada
Lauyan Najeriya Malcolm Omirhobo ya bayyana cewa ba zai janye karan daya shigar kam hana matan Musulmai sanya Hijabi ba. Lauyan ya shigar da kara uku kan Musulunci na farko hana mata sanya hijabi sai kuma cire yaren larabci a jikin nira da kuma jikin kakin sojoji. Inda ya jadadda cawa shi na zai janye karan nasa domin hakkin ne shine yake bi. A baya lauyan yayi shiga irin ta juju yaje kotu wanda hakan yasa mutane ke cewa yayi shigar ne don zanga zang akan amincewa matan Musulmi sanya hijabi.
Kungiyar Musulmai ta fadawa lauya Malcolm cewa ya janye karan daya shigar kan hana mata saka hijjabi da cire yaren larabci a jiki kaakin soji da kuma Naira

Kungiyar Musulmai ta fadawa lauya Malcolm cewa ya janye karan daya shigar kan hana mata saka hijjabi da cire yaren larabci a jiki kaakin soji da kuma Naira

Ibada
Kungiyar MURIC dake kare hakkin Musulmai tayi kira ga lauya Chief Malcolm Omirhobo wanda yayi shigar Juju zuwa kotu bayan kotun ta amincewa matan musulami su riga saka hijjabi. Amma lauyan ya kare kansa yace shi ba zanga zanga ce kan amincewa matan musulmai su riga saka hijjabi ce tasa yayi wannan shigar ba. Lauya ya maka Musulmai a kotu cewa ta hana mata saka hijjabi sannan kuma ta cire yaren larabci a jikin Naira da kuma kakin sojoji. Amma shugaban kungiyar Musulman, Farfesa yayi kira ga lauyan cewa ya janye karan nasa tunda yace shi bai tsani musulmai kuma bai son tada zaune tsaye bane.
Allahu Akbar: Wani malamin jami’ar Gombe ya rasu a kasa mai tsarki

Allahu Akbar: Wani malamin jami’ar Gombe ya rasu a kasa mai tsarki

Ibada
Kungiyar mahajjatan jihar Gombe ta bayyana mutuwar Dr. Abdulrahnan mai Gona a kasa mai tsarki yau ranar alhamia, wanda ya kasance malami a jami'ar jihar. Kungiyar tace Abdulrahman ya kasance malami a sashen addinin musulunci kuma tace ya mutu ne bayan yayi jinya kan kankanuwar rashin lafiya. Mai Gona ya kasance daya daga cikin mutanen da gwamnan jihar Muhammad Yahana Inuwa ya biyawa kudin hajji domin ziyartar kasa mai tsarki. Kuma kungiyar mahajjatan ta kara da cewa za a yi masa jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Gwamna Ganduje ya gargadi ‘yan siyasa cewa kar su sake suyi kamfe a farfajiyar Sallar Idi

Gwamna Ganduje ya gargadi ‘yan siyasa cewa kar su sake suyi kamfe a farfajiyar Sallar Idi

Ibada, Siyasa
Gwamnan jihar Kano Abdullhi Ganduje ya gargadi 'yan takarar dake yin kamfe a farfajiyar Sallahr Idi yace hakan ya sabawa kundin tsafin mulkin Najeriya. Inda ya jaddada cewa ya hana hakan kar wani dan takara ya bayyana fastocinsa a wurin Sallar ko kuma yayin da ake Hawan Daushe. Gwamnan jihar ya bayyana hakan ne a wata wasikar data fito daga hannun kwamishinan sadarwa na jihar, watau Mallam Muhammad Garba.