Da Duminsa: Farashin litar man fetur ya kai Naira 937 a jihar Jigawa
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa, Farashin Litar mai a jihar ya kai naira 937.
Hukumar kididdiga ta kasa,NBS ce ta bayyana haka a bayanan da ta fitar na farashin man fetur a watan Mayu.
Hakan ya nuna ci gaba da tashin farashin man fetur din tun bayan cire tallafin man fetur.
A cikin jihohin Najeriya,Jihar ta Jigawa itace ke da farashin man fetur mafi tsada sai jihar Ondo na take mata baya da farashin 882.67 sannan sai jihar Benue me farashin 882.22