Sunday, July 21
Shadow

Kara Kiba

Danyen kwai yana kara kiba

Kara Kiba
A kimiyyar Lafiya, danyen Kwai baya kara kiba, maimakon amfani,shan danyen kwai zai iya haifar da matsalar lafiya. Wani abu da ba kowa ya sani ba shine, dafaffen kwai wanda aka tafasa,yafi danyen kwai yawan sinadaran protein. Abinda aka sani game da cin kwai dan kara lafiyar jiki shine a rika cin guda daya ko biyu a kullun. Shan danyen kwai yana da hadarin sanya cutar amai da gudawa, Zazzabi da ciwon gabobi. Dan haka idan neman kiba ake wajan shan danyen kwai a dena. Akwai kayan abinci da yawa da ake amfani dasu dan samun kiba ta hanyar lafiya maimakon shan danyen kwai me hadari. Kayan abinci irin su madarar ruwa, kankana, Ayaba, Madarar Waken Suya, Madarar Kwakwa duk suna sanya a yi kiba, dan karanta cikakken bayani kan abincin dake sanya kiba a karanta Abincin dake ra...

Kunun kara kiba

Kara Kiba
Ana hada kunun karin kiba dan sha a samun kiba musamman ga wadanda suke da rama wadda ta wuce kima. Ga yanda ake hada Kunun kara kiba kamar haka: Ana samun madarar waken suya kofi 1, sai a hadata da ruwan mangwaro da aka matse, sai a samu ayaba daya a saka a markada. A sha sau daya a rana ko kuma gwargwadon yanda ake son yin kiba, cikin sati guda za'a ga mamaki. Ana kuma iya hada Apple, Dabino, Kwakwa, Ayaba, Madara ta ruwa, madara ta gari, Abarba, citta. A yi blending a rika sha akai-akai.

Hanyoyin kara kiba

Kara Kiba
Kara kiba musamman me tsabta ba wadda zata wuce kima ba na da kyau. Saboda rama wadda ta wuce kima na iya zama matsala wadda zata sa ka rasa abubuwan kariya na jiki da zasu iya kaiwa ga raguwar karfin jiki ta yanda zaka rika karyewa cikin sauki. Ga hanyoyin da za'a kara kiba cikin sauki: A kara yawan abincin da ake ci, a rika cin abinci kadan-kadan a lokuta daban-daban a rana. A rika shan madara, madara na taimakawa sosai wajan karin kiba me tsafta. A rika cin kifi da kwai da wake. A rika shan yegot, A ci chakulate a sha ice cream daidai gwarwado. Rika motsa jiki. A rika cin soyayyen dankalin Hausa dana Turawa da kwai. A rika cin naman kaza. A rika cin bindin rago, ko na sa. A rika cin doya, Madarar Kwakwa. Kar a sha ruwa kamin a ci abinci, saboda haka...