
Farashin gangar danyen Man Amurka ya fadi zuwa Dala 1, Na Duniya kuma ya fadi zuwa Dala 26
Kasuwar Danyen mai ta Duniya na ci gaba da tangal-tangal inda farashin man ke ci gaba da faduwa duk da rage yawam man da kungiyar kasashen OPEC suke hakowa suka yi.
Masana sun bayyana cewa dalilin da yasa man ya fmci gaba da faduwa shine saboda zaman gida da miliyoyin mutane ke yi a kasashe masu Arziki saboda cutar Coronavirus.
Bukatar man dai ta ragu sosai inda farashin danyen man na Amurka ya fadi zuwa kasa da Dala 0. Sannan farashin na Duniya, wanda dashine akewa man Najeriya farashi ya fadi zuwa Dala 26.