fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Kasuwanci

Banki Musulunci yana da amfani sosai – Sanusi Lamido Sanusi

Banki Musulunci yana da amfani sosai – Sanusi Lamido Sanusi

Kasuwanci
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Alhaji Muhammadu Sanusi, ya zargi wasu ‘yan Najeriya da yin amfani da addini domin a boye gaskiya. Ya yi magana a kan cece-kucen da ya biyo bayan bullo da tsarin hada-hadar kudi da babu ruwa wanda aka fi sani da bankin Musulunci. Sanusi, wanda ya kasance bako a wajen taron harkar kasuwanci na kasa a karo na 5, wanda kungiyar musulmi maza masu sha’awar kasuwanci da sana’o’i da suka gudanar a jami’ar Legas, ya ce babban bankin CBN ya yi kokarin bayyana wa mutane cewa babu wani abu kamar mayar da kirista Musulmai a cikin bankin Musulunci a kasar nan. Sai dai ya ce babban bankin na CBN ba zai iya tsayawa ba saboda ‘yan kalilan din da suka ki sauraron bayanin bankin koli, yana mai cewa alfanun tsarin bankin Musulunci na da yawa....
Katar Airways ta kaddamar da yin jigila a Kano

Katar Airways ta kaddamar da yin jigila a Kano

Kasuwanci
Jirgin na farko na Qatar Airways ya sauka a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, MAKIA. Jirgin ya sauka ne cikin farin ciki da ga masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jirgin, Boeing 787 Dreamliner, ya sauka a filin jirgin da misalin karfe 11:10 na safe. Jami’an hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama na tarayyar Najeriya FAAN ne su ka tarbe jirgin ta hanyar fesa masa ruwa kamar yadda a ka saba. Jirgin na Qatar zai fara jigilar fasinjoji zuwa Kano a wani bangare na shirin fadada kasar. Hakan zai biyo bayan Fatakwal, Jihar Ribas ranar Alhamis. Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Jami’an Gwamnatin Jihar Kano da Kamfanin Jiragen Sama na Qatar Airways da dai sauransu sun tarbi Jirgin Qatar Airways zuw...
Karya ake mana: Ba sayar da shinkafar da muka kwace daga hannun ‘yan kasuwa ba muke>>Inji hukumar Kwastam

Karya ake mana: Ba sayar da shinkafar da muka kwace daga hannun ‘yan kasuwa ba muke>>Inji hukumar Kwastam

Kasuwanci
Hukumar Kwastam ta bayyana cewa basa sayar da shinkafar da suka kwace daga hannun 'yan kasuwa.   Tace duk rade radin da ake akan hakan ba gaskiya bane.   Tace idan shinkafar da suka kwace me kyauce, zasu baiwa 'yan gudun hijira, idan kuma ba mai kyau bace, to zasu baiwa masu gidajen kaji.   Daya daga cikin kwamandan Kwastam, Dera Nnadi ne ya bayyana haka.
Arzikin Dangote ya ƙaru da dala biliyan biyu

Arzikin Dangote ya ƙaru da dala biliyan biyu

Kasuwanci
Arzikin Aliko Dangote ya ƙaru matuƙa yayin da yake yunƙurin kammala shekarar 2021 da arzikin da bai taɓa samu ba cikin shekara bakwai sakamakon haɓakar ribarsa a ɓangaren siminti. Haɓakar kasuwar hannun jari a kamfaninsa na siminti da kuma tashin farashin man fetur da takin zamani sun taimaka wa Dangote inda dukiyarsa ta ƙaru da dala biliyan 2.3 a 2021 zuwa biliyan 20.1 jumilla, kamar yadda mujallar Bloomberg ta ruwaito. Rabon da dukiyarsa ta kai yawan haka tun 2014, lokacin da ta kai dala biliyan 26.7 a watan Yunin shekarar, a cewar jaridar. Tashin farashin kayayyakin gini a Najeriya, wadda ke da mafi girman tattalin arziki a Afirka, sun haɓaka ƙarfin jarin kamfanin Dangote Cement plc. Nan gaba kaɗan ake sa ran Dangote zai kammala ginin matatar man fetur kan dala biliyan 19, wadda z...
Bamu da iko akan farashin Gas din girki>>Gwamnatin Tarayya

Bamu da iko akan farashin Gas din girki>>Gwamnatin Tarayya

Kasuwanci
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa bata da iko akan farashin gas din girki dake ta hauhawa.   Shugaba Buhari ya bayyana damuwa kan lamarin, kuma farashin gas din na tafiyane da farashin da ake amfani dashi a Duniya.   Karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva ne ya bayyana haka inda yace gwamnati ta tsame hannunta daga harkar gas dan haka ba itace ke kula da farashinsa ba.
Masu zuba jari na kasashen waje sun kauracewa Najeriya

Masu zuba jari na kasashen waje sun kauracewa Najeriya

Kasuwanci
Samun masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Najeriya yayi kasa da kaso 80 a cikin shekaru 2 da suka gabata.   Kudaden da masu zuba jari daga kasashen waje a Najeriya ya fadi daga dala biliyan $17.1 zuwa a shekarar 2019 zuwa dala biliyan $3.4 a shekarar 2021.   Babban bankin Najeriya,  CBN ne ya fitar da wannan alkaluma inda ya danganta zuwan cutar coronavirus da hakan.   Amma masana da masu sharhi akan alkaluman tattalin arziki sun bayyana matsalolin tsaro dana hauhawar farashin kayayyaki da yawan hawa da tashin kudin Najeriya ga hakan.
Kasar Libya ta shiga gaban Najeriya inda ta zama kasa ta daya a Africa wajan fitar da man fetur

Kasar Libya ta shiga gaban Najeriya inda ta zama kasa ta daya a Africa wajan fitar da man fetur

Kasuwanci
Rahotannin da muke samu na cewa Najeriya ta rasa matsayinta da ta dade tana rike dashi na zama kasa ta daya a Africa wajan fitar da danyen Man fetur.   Yawan man da Najeriya ke fitarwa yayi kasa saboda dalilai da yawa, hutudole ya fahimta a rahoton da kungiyar OPEC ta fitar.   Yawan man da Najeriya ke fitarwa ya koma ganga Miliyan 1.23 a kullun, kamar yanda hutudole ya fahimta a rahoton watan October da aka fitar.   Tun a watan Disambar shekarar data gabata ne dai kasar Libya ta zarta Angola inda ta zama ta 2 wajan fitar da danyen man, kamar yanda hutudole ya fahimta, hakanan kuma gashi yanzu yawan man da take fitarwa ya kai ganga miyam 1.24 kullun, Kumar yanda yake a Rahoton OPEC da hutudole ya hango.
Ba a Najeriya bane kadai, Farashin kayan abinci ya yi tashi mafi girma a duniya cikin shekara 10>>MDD

Ba a Najeriya bane kadai, Farashin kayan abinci ya yi tashi mafi girma a duniya cikin shekara 10>>MDD

Kasuwanci, Uncategorized
Farashin abinci a duniya ya yi tsadar da bai taba yi ba cikin shekara 10 bayan tashin da ya yi da kashi 30 cikin 100 a bara, in ji hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO). Alƙaluman hukumar sun nuna yadda farashin hatsi da na kayan miya da mai ya yi tashin gwauron zabi a duniya. Man da ake tatsa a jikin kayan miya ya tashi da kashi 10 cikin 100 a watan Oktoba. Yankewar da aka samu wajen kai kayayyaki, da tashin farashin kayan amfanin yau da kullum, da rufe ma'aikatu da kuma rikicin siyasa, sun taimaka wajen tashin farashin. FAO ta ce ma'aunanta sun nuna farashin hatsi ya tashi da sama da kashi 22 idan aka kwatanta da farkon wannan shekarar. Farashin dawa na daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen wannan hauhawa, inda ya karu da kashi 40 a wat...
MTN na rabawa ‘yan Najeriya Data kyauta: Ka samu taka kuwa?

MTN na rabawa ‘yan Najeriya Data kyauta: Ka samu taka kuwa?

Kasuwanci
Kamfanin sadarwa na MTN ya raba wa kwastamominsa katin waya da data kyauta a matsayin diyya sakamakon matsalar da ya samu a makon da ya gabata. Shugaban kamfanin MTN ne Karl Toriola ya tura wa masu amfani da MTN saƙon a ranar Lahadi tare da wani adireshin YouTube inda ya nemi afuwa kan katsewar sadarwa da ya samu. Sakon na cewa “an dawo maka da katinka na waya da kuma data da ka yi amfani tsakanin 12 zuwa 7 na yamma. A cikin sakon, shugaban MTN ya ce injiniyoyin kamfanin sun fahimci cewa an samu matsalar ne daga wata tangardar na’ura da ta mayar da kwastamomi daga tsarin 4G zuwa 3G wanda ya haifar da katsewar layukan na MTN. Ya ce yanzu an magance matsalar.