fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Kasuwarmu/Sponsored

SAYI LITTAFIN: DABARUN KASUWANCI A ZAMANI

SAYI LITTAFIN: DABARUN KASUWANCI A ZAMANI

Kasuwarmu/Sponsored
DABARUN KASUWANCI A ZAMANI Littafine dake cike da Sabbin Dabaru na Kasuwanci, tare da bayani Dangane da Kasuwanci hadi da Bayani akan Wasu dabarun da ake bi wajan Kafa Masana'anta da Jari kankani, haka Zalika littafin yayi duba sosai akan Dabarun Fara Sana'o'i ga wanda Yake son Farawa, dama wanda Yake neman wata Sahihiyar hanyar da zai juya kudinsa domin Zama Dankasuwa mai cikakken iko. https://selar.co/6mq4
Shugaba Buhari ya karbi bakuncin mai kamfanin BUA a fadarsa

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin mai kamfanin BUA a fadarsa

Breaking News, Kasuwarmu/Sponsored
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a yau ranar juma'a shuwagabannin kamfanin BUA suka kai masa ziyara a fadarsa dake babban birnin tarayya. Shugaba Buhari da kansa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter. Inda yace shugaban kamfanin Abdulsamad Rabiu ne ya jagoranci tawagar tasa kuma ya matukar ji dadin wannan ziyarar tasu. Buhari ya yace Najeriya na matukar alfahari da kamfanin nasu domin yana kawo mata cigaba sosai.
Mai kudin Duniya, Elon Musk ya sayar da hannun jarinsa na dala biliyan 6.9 na kamfanin Telsa, shin ko meye dalili?

Mai kudin Duniya, Elon Musk ya sayar da hannun jarinsa na dala biliyan 6.9 na kamfanin Telsa, shin ko meye dalili?

Breaking News, Kasuwarmu/Sponsored, Uncategorized
Mai kudin duniya, Elon Musk ya sayar da hannun jarinsa na dala biliyan 6.9 na shahararren kamfanin motar Telsa. Musk ya sayar da wannan hannun jarin nasa ne kan maka shi a kotu da kamfanin sada zumunta ta Twitter tayi. A baya Elon Musk ya taya kamfanin sada zumuntar ta Twitter a farashin dala biliyan 44 amma sai yasa fasa kan akwai wasu asusu na bogi da yawa a ciki. Wanda hakan ne yasa masu kamfanin suka fusata suka maka shi a kotu, inda za a saurari shari'ar a ranar 17 ga watan Augusta. Kuma Musk yace ya sayar da wannan hannun jarin nasa ne koda watakila idan ya fadi shari'ar sai ya saya kafar sada zumuntar. Yayin da kuma har yanzu dai yake da hannun jari a kamfanin motar na miliyan 155.04.
Daga yanzu kamfanin NNPC zai riga samarwa kansa riba bayan an saka hannun jarin biliyan 200 a cikinsa, cewar Muhammadu Buhari

Daga yanzu kamfanin NNPC zai riga samarwa kansa riba bayan an saka hannun jarin biliyan 200 a cikinsa, cewar Muhammadu Buhari

Breaking News, Kasuwarmu/Sponsored, Siyasa
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a yau ya kaddamar da sabon kamfanin NNPC Limited a babban birnin tarayya Abuja. Shugaban kasar ya kara da cewa 'yan kasuwa sun saka hannun jarin biliyan 200 a sabon kamfanin. Kuma daga yanzu yace kamfanin zai riga sanarwa kansa riba ba tare da tallafin gwamnati ba. Sannan yanzu zai cigaba da aiki ne kamar kamfani mai zaman kansa ba ba tare da takura ba.
Ina alhafari daya kasance a mulkina aka samu cigaban harkar man fetur wanda zai samar tsaro kuma ta habaka tattalin arzikin Najeriya, cewar shugaba Buhari

Ina alhafari daya kasance a mulkina aka samu cigaban harkar man fetur wanda zai samar tsaro kuma ta habaka tattalin arzikin Najeriya, cewar shugaba Buhari

Breaking News, Kasuwarmu/Sponsored, Siyasa
Shugaban kasar Najeriya, Mejo Janar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana alfahari daya kasance a mulkinsa ne aka samu cigaban harkar man fetur wanda zai samar da tsaro kuma ya habaka tattalin arzikin Najeriya. Shugaban ya bayyana hakan ne bayan ya kaddamar da sabon tsarin kasuwanci a kamfanin NNPC Limited a babban birnin tarayya Abuja yau. Inda yace wannan sabon tsarin na kasuwanci zai kawo cigaba sosai a kasa kuma harkar mai zata kara daukaka sannan kasar Najeriya zata tsaro sosai.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tsokaci kan sayar da kamfanin NNPC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tsokaci kan sayar da kamfanin NNPC

Breaking News, Kasuwarmu/Sponsored, Siyasa
Rahotanni da dama sun bayyana cewa shugabam kasar Majeriya ya sayar da kamfanin man fetur na kasa NNPC. Amma yanzu hadiminsa Tolu Ogunlesi ya karyata rahotannin dake bayyana cewa gwamnatin ta sayar da kamfanin NNPC, yace har yanzu kamfanin gwamnati ne. A karshe yace shugaba Buhari ya mayar da kanfanin na kasuwanci ne kawai amma bai sayar dashi ba har yanzu mallakin gwamnati ne. A yau shugaban kasar ya hallacin gagarumin taron daya kaddamar da kamfanin NNPC zuwa NNPCL na kasuwanci a babban birnin tarayya Abuja.
Gwamnatin tarayya ta amincewa ‘yan kasuwar man fetur sun kara farashin lita

Gwamnatin tarayya ta amincewa ‘yan kasuwar man fetur sun kara farashin lita

Kasuwarmu/Sponsored, Siyasa
Gaamnatin tarayya ta amincewa 'yan kasuwar man fetur sun kara farashin litar man  daga 165 zuwa 179. Manema labarai na DailyTrust ne suka ruwaito wnnan labarin kuma dama tun kafin gwamnatin tarayyar ta amince wasu daga cikinsu basa sayarsa akan naira 165. Inda wasu ke sayarwa akan 170 zuwa 180 har 190 ma wasu 'yan kasuwar na sayar da man fetur din. Kuma duk da haka dai hukumar dake lura da harkar man fetur ta NMDPRA batayi tsokaci akan kara farashin litar man ba.