Monday, December 2
Shadow

Hawan Jini

Alamomin hawan jini

Duk Labarai, Hawan Jini
A mafi yawan lokuta, hawan jini baya nuna wata alama da zata tabbatar mutum ya kamu dashi. Saidai yana kara hadarin kamuwa da cutar zuciya, Shanyewar rabin jiki, da sauran matsaloli masu yawa. Menene Hawan Jini? Hawan Jini yana nufin idan jinin mutum ya taru yayi yawa fiye da yanda ya kamata, wanda hakan zai sa Zuciyar mutum ta yi aiki fiye da yanda ya kamata. Hawan jini, wanda aka fi sani da "high blood pressure" a Turance, yanayi ne da ake samun karuwar matsa lamba na jini a jikin mutum. Wannan yanayi na iya zama mai hadari domin yana iya haifar da matsaloli masu yawa kamar su bugun zuciya, bugun jini (stroke), da sauran matsalolin lafiyar zuciya. Ana auna hawan jini ta hanyar amfani da lambobi biyu, wanda ake kira systolic (lambobin farko) da diastolic (lambobin ƙarshe)...