Saturday, June 6
Shadow

Kiwon Lafiya

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Bauchi ya ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Bauchi ya ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa gwamnan Bauchi,  Sanata Bala Muhammad ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.   https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1242479926793523206?s=19   Hakan ya bayyanane ta hannun bashir Ahmad hadimin shugaban kasa.   A cikin sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, mutane 6 ne aka gwada akan cutar ta Coronavirus/COVID-19 bayan da gwamnan Bauchin ya sha hannu da dan Atiku daya kamu da cutar a haduwar da suka yi a jirgin sama.   Cikin mutane 6 akwai iyalan gwamnan da hadimansa da da suka mai rakiya zuwa legas kuma duk basu dauke da cutar sai shine gwamnan kadai aka sami da ita. https://twitter.com/LadanSalihu1/status/1242481017044307969?s=19 Gwamnan yayi rokon cewa a sakashi cikin addu'a sannan yana kira ga duk wa
Coronavirus ta kashe mutum na farko a Saudiyya

Coronavirus ta kashe mutum na farko a Saudiyya

Kiwon Lafiya
Saudiyya ta tabbatar da mutum na farko da ya mutu a kasar sakamakon coronavirus. Ma'aikatar lafiya ta kasar ta shaida cewa wanda cutar ta kashe dan asalin kasar Afghanistan ne kuma mai shekaru 51. Saudiyya ita ce kasar da ta fi yawan masu cutar a Gabas ta Tsakiya bayan Iran. A ranar Talata an samu karin masu dauke da cutar da mutum 205 inda yawansu a halin yanzu ya kai 767. Kasar ta saka tsatsauran matakai ciki har da dokar hana fita ta makonni uku domin kokarin dakile yaduwar cutar.
An dakatar da al’amura a fadar shugaban kasa, za’a kai Abba Kyari Legas dan dubashi

An dakatar da al’amura a fadar shugaban kasa, za’a kai Abba Kyari Legas dan dubashi

Kiwon Lafiya
Rahotanni daga fadar shugaban kasa na cewa, an tsayar da ayyukan fadar cak bayan da aka samu shugaban ma'aikata na shugaban kasa,Abba Kyari dauke da cutar.   Rahoton yace shugaban ma'aikatan yayi mu'amala da mutane da yawa a fadar bayan dawowarshi daga kasashen Jamus da Egypt wanda hakan yasa wasu daga cikin wanda yayi ma'amala dasu suka killace kansu.   Sahara Reporters tace Abba Kyari yayi mu'amala da me magana da yawun shugaban kasa,Garba Shehu da kuma me baiwa shugaban kasar shawara kan harkar tsaro, Babagana Monguno dadai sauransu kuma ana tunanin sun killace kansu.   Hakanan Abba Kyari yayi mu'amala da gwamnan Kogi, Yahaya Bello a yayin da ya jewa gwanan gaisuwar mahaifiyarsa da ya rasu.   Ana tsammanin gwamna Bello shima ya killace kansa. ...
Uwargidan Shugaban Kasa Ta Hana Kowa Ganin Shugaban Buhari, bayan Abba Kyari ya kamu da Cutar Coronavirus/COVID-19

Uwargidan Shugaban Kasa Ta Hana Kowa Ganin Shugaban Buhari, bayan Abba Kyari ya kamu da Cutar Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta haramtawa kowa shiga fadar Shugaban kasa, domin ganin Buhari, biyo bayan shugaban ma’aikatan fadar Abba Kyari da ake zargin ya kamu da cutar Coronavirus kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito.     Kafofin watsa labarai sun ba da rahoton cewa an gwada Mr Kyari ya kamu da cutar COVID-19.     A wani rahoto da jaridar ThisDAY, ta fitar ta ce Mista Kyari ya kamu da cutar yayin da ya ziyarci Jamus a ranar Asabar, 7 ga Maris, don ganawa da jami’an Siemens a Munich kan shirin fadada wutar lantarki na Najeriya.     A sanadin haka, Uwargidan Shugaban Kasa ta fitar da sanarwar sababbin tsare-tsaren gida ga Shugaban kasa.     Uwargidan Shugaban kasa ba ta barin kowa ya ga Shuga
Wani Mutum da ya dawo daga Kasar Thailand yaki killace kansa yana yawo a Kano

Wani Mutum da ya dawo daga Kasar Thailand yaki killace kansa yana yawo a Kano

Kiwon Lafiya
Bayan maganar mutuminnan da aka yi ta rade-radin cewa yana dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 a cikin wani jirgi da ya je Kano daga Legas wanda a karshe aka gano cewa be taba hawa jirgi bane kuma cutar Malariya ce ke damunsa.   An samu wani mutun shima da ake zargin ya dawo ne daga kasar Thailand ya kuma biyo ta Legas ya koma Kano.   Rahoton yace mutumin yaki killace kansa kuma yana shiga gari abinshi harma ana zargin ya shiga kasuwa.   Wani bawan Allah ne ya aikewa hadimin gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai da wannan sako inda yayi kiran da a kaiwa jama'a dauki a je a duba mutuminnan. https://twitter.com/dawisu/status/1242410986503573505?s=19 Yakasai ya baiwa mutumin tabbacin cewa zai kai wannan korafi gaba dan daukar matakin daya dace.  
Wata sabuwa an sake samun bullar wata cutar a Chaina mai suna Hantavirus

Wata sabuwa an sake samun bullar wata cutar a Chaina mai suna Hantavirus

Kiwon Lafiya
A yayin da duniya ke fafutukar yakar cutar Covid-19 sai gashi labarai ya sake iske mu da cewa wata cuta mai suna Hantavirus ta sake bullowa daga kasar Chaina, kamar yadda Global Time suka bayyana. Mutumin da ya kamu da wannan cuta dan yankin Yunnan ne, inda aka rawaito mutumin ya mutu a lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa zuwa lardin Shandong dan aiki, an rawaito cewa mutumin yayi wannan tafiya ne a cikin motar haya, inda daga bisani aka tabbatar da kamuwarsa daga wannan cuta ta Hantaviru. An kuma gwada mutum 32 wanda suka kasance da mutumin a cikin mota. Cutar Hantavirus na da alaka da dangin su bera.
Karin haske kan jirgin daya sauka a Kano daga Legas direban jirgin ya ki bude kofa saboda ana zargin akwai me Coronavirus/COVID-19 a ciki

Karin haske kan jirgin daya sauka a Kano daga Legas direban jirgin ya ki bude kofa saboda ana zargin akwai me Coronavirus/COVID-19 a ciki

Kiwon Lafiya
Wani jirgin Air Peace daya sauka a Kano  daga Legas amma matukin jirgin yaki bude kofar saboda ana tunanin akwai me dauke da Coronavirus/COVID-19 a ciki ya dauki hankula sosai musamman a shafukan sada zumunta.   Bidiyon jirgin da yanda lamarin ke faruwa ya watsu a shafukan sada zumunta sosai inda akai ta yabawa matukin jirgin saboda kin bude kofar.   https://twitter.com/AliGrema/status/1242402861457313792?s=19   Mutumin da ake zargin yana dauke da Coronavirus/COVID-19 a cikin jirgin yayi ta kwarara amaine   Saidai bayan zuwam jami'an hukumar kula da cututtuka ta Najeriya,  NCDC kuma aka duba wannan fasinja dake zargi yana dauke da cutar an tabbatar cutar zazzabin Maleriya ne ke damunsa kuma an tsaftace dukkan fasinjojin dake jirgin sannan an dauk
Shugaban ma’aikatan Buhari, Abba Kyari ya kamu da Coronavirus/COVID-19 saidai NCDC ta yi magana

Shugaban ma’aikatan Buhari, Abba Kyari ya kamu da Coronavirus/COVID-19 saidai NCDC ta yi magana

Kiwon Lafiya
Rahotannin dake fitowa daga fadar shugaban kasa na cewa shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasar, Abba Kyari ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.   Rahoton yace Abba kyari yayi gwani kuma gwajin ya nuna cewa yana dauke da cutar kamar yanda Thisday ta ruwaito.   Dalilin hakane yasa aka gwada Shugaban kasa,Muhammadu Buhari shima akan cutar inda shi kuma sakamakon ya nuna cewa bashi da ita.   Abba Kyari yayi tafiya zuwa kasar Jamus a ranar Asabar, 7 ga watan Maris inda ya gana da wasu kamfanonin kan habaka wutar Najeriya.   Saidai da Daily Post ta tambayi hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC tace bata fitar da sanarwar cutar akan mutum daya sai ta tsaya ta yi bincike tukuna sannan kuma bata bayar da sunayen mutanen da suka kamu da cutar.