fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta baiwa ma’aikatanta hutu sai abinda hali yayi

Gwamnatin tarayya ta baiwa ma’aikatanta hutu sai abinda hali yayi

Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta baiwa ma'aikatanta hutu inda tace ma'aikata da bana aiki na musamman ba daga mataki na 12 zuwa kasa su zauna a gida.   Sanarwar daga shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya tace ma'aikatan su ci gaba da aiki daga gida.   Ta kuma basu shawarar bin ka'idojin da aka gindaya dan yaki da cutar watau nesantar tarukan jama'a da kuma tsafta.   Tace ma'aikatan da zasu rika zuwa aiki kuma su tabbatar sun tsagaita yawan mutanen da zasu rika gani.   Sanarwar bata bayyana ranar dawowa aiki ba inda tace har sai abinda hali yayi
Ma’aikacin FIRS ya bayyana cewa ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19

Ma’aikacin FIRS ya bayyana cewa ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Wani Ma'aikacin hukumar dake kula da karbar Haraji ta kasa, FIRS me suna Salihu Umar ya bayyana cewa ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.   Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumuntar Twitter inda yace ya sanar da jami'an lafiya.   A lokacin da yake rubuta sakon yace suna kan hanyar zuwa gida su tafi dashi.     A baya dai hukumar ta FIRS ta karyata cewa babu ma'aikacinta ko daya dake dauke da cutar.    
Mikel Arteta ya warke daga coronavirus

Mikel Arteta ya warke daga coronavirus

Kiwon Lafiya
Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce ya warke sarai daga coronavirus da ya kamu da ita.     Dan kasar Spaniya, mai shekara 37, ya zama kocin Premier na farko da ya kamu da coronavirus ranar 12 ga watan Maris.     Kocin ya sanar da baya jin dadin jikinsa, bayan da aka tabbatar ya yi cudanya da mai Olympiokos, Evangelos Marinakis wanda ya kamu da cutar ranar 10 ga watan Maris, inda Arsenal ta buga Europa League da kungiyar ta Girka.     Arteta ya ce ''Sai da na yi kwana uku zuwa hutu ina jinya sannan na fara jin karfin jikina, daga nan alamun cutar ya bace''     Ranar Talata ya kamata 'yan wasan Arsenmal su koma atisaye, bayan da aka killacesu mako biyu, saboda samun Arteta da coronavirus, an kuma dage ranar da za su koma...
Coronavirus: Gwamnatin Jihar Borno ta hana zuwa matsugunin ‘yan gudun hijira na tsawon makonni 4

Coronavirus: Gwamnatin Jihar Borno ta hana zuwa matsugunin ‘yan gudun hijira na tsawon makonni 4

Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Borno ta dakatar da ziyara zuwa mazaunan masu gudun Hijira a jihar har nan da sati 4.   Gwamnatin ta dauki matakinne saboda dakile matsalar yaduwar cutarnan ta Coronavirus.   Shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, Hajiya Yabawa Kolo ce ta tabbatar da haka inda tace daukar matakin ya zama Dole lura da yanda cutar Coronavirus ta shiga kasahen Chadi da Kamaru dake makwabtaka da jihar.   Tace kasahen da suka ci gabama da cutar ta shiga sun kasa kula da jam'arsu ballanatana mu.   Tace dan haka sun hana karbar karin 'yan gudun hijira har nan da sati 4 tukuna.    
Yanzunnan:Gwamnatin tarayya ta kulle iyakokin Najeriya na kasa nan da zuwa Sati 4

Yanzunnan:Gwamnatin tarayya ta kulle iyakokin Najeriya na kasa nan da zuwa Sati 4

Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta sanar da rufe iyakokin kasa na Najeriya daga nan zuwa saki 4 saboda maganin yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.   Wannan na kunshene cikin sanarwar da sakataren gwamnatin tarayya Bos Mustapaha wanda kuma shine jagoran kwamitin shugaban kasa kan yakar cutar ya bayyanar.   https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1242152389618130951?s=19   Gwamnatin Najeriya na kara kaimi wajan ganin ta dakile duk wani abu da zai kawo yaduwar cutar ta Coronavirus/COVID-19.
Najeriya na iya amfani da sojoji, ‘yan sanda don tilastawa jama’a nisantar juna

Najeriya na iya amfani da sojoji, ‘yan sanda don tilastawa jama’a nisantar juna

Kiwon Lafiya
Najeriya na iya amfani da sojoji, 'yan sanda don tilasta nisantar da jama'a Gwamnatin Najeriya a ranar Litinin ta bayyana cewa zata iya amfani da sojoji da sauran jami'an tsaro don dakile kara ya duwar cutar Covid-19 a fadin kasar. Ministan yada labarai na kasar, Lai Mohammed ne ya bayyana haka, ya ce wannan zai taimaka wajen dakatar da yaduwar cutar. Ya zuwa yanzu dai Najeriya ta tabbatar da sabbin masu dauke da cutar har guda tara a yau da kuma mutuwar mutum guda daya. Ya zuwa yanzu, kasar ta tabbatar da wanda suka kamu sun kai guda 39.
Coronavirus/COVID-19: Babban masallacin Abuja ya dakatar da Salloli 5 data Juma’a

Coronavirus/COVID-19: Babban masallacin Abuja ya dakatar da Salloli 5 data Juma’a

Kiwon Lafiya
Hukumar masallacin kasa dake babban birnin tarayya Abuja ta sanar da dakatar da salloli 5 da sallar Juma'a.   Hakan na kunshene a cikin sanarwar da masallacin ya fitar da tace wannan mataki zai fara aikine daga yau,Litinin 23 ga watan Maris 2020. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1242113890265305089?s=19 Masallacin yace an dauki wannan matakine dan magance yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.    
Gwamnatin Kaduna ta rufe kasuwa ta baiwa ma’aikata hutu

Gwamnatin Kaduna ta rufe kasuwa ta baiwa ma’aikata hutu

Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Kaduna ta baiwa ma'aikatan jihar hutun kwanaki 30 dalilin Coronavirus/COVID-19 inda hakan kokarine na kare yaduwar cutar   Gwamnan Kadunan,Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter inda yace ma'aikata daga mataki na 12 su zauna a gida har nan da kwanaki 30.   Gwamnan yace masu bayar da aiki na musamman ne kawai zasu rika zuwa aiki.   Sannan ya kara da cewa a kasuwa ma masu sayar da magani da abinci kadai ake son su fito. https://twitter.com/GovKaduna/status/1242091369088397314?s=19
Ko kunsan wanene mutumin da Coronavirus/COVID-19 ta kashe a Najeriya?

Ko kunsan wanene mutumin da Coronavirus/COVID-19 ta kashe a Najeriya?

Kiwon Lafiya
Rahotanni daga Jihar Legas sun tabbatar da mutuwan Tsohon Manajan Darakta na Hukumar PPMC me suna Mista Sulaiman Achimugu.     Mr. Achimugu wanda ya dawo daga kasar Landan makonni biyu ya fara nuna alamar cutar inda aka killace shi zuwa wani lokaci karkashin kulawan likitoci daga karshe yace ga garin su.     Hukumomi sun tabbatar da mutuwan Achimugu sanadiyar cutar CoronaVirus
Coronavirus/COVID-19: Gwamnan jihar Bauchi ya killace kansa

Coronavirus/COVID-19: Gwamnan jihar Bauchi ya killace kansa

Kiwon Lafiya
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya killace kansa tun bayan hada jirgi da ya yi da dan gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar wanda ya kamu da cutar coronavirus.   Mai magana da yawunsa, Ladan Salihu ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter. https://twitter.com/LadanSalihu1/status/1242055883699429382?s=19 Ladan ya ce "mun hau jirgi daya da dan gidan na Atiku daga Lagos zuwa Abuja, inda suka yi musabiha hannu da hannu. Tuni aka yi wa gwamna da mu 'yan tawagarsa gwaji. Muna fatan sakamakon gwajin zai yi kyau."