
Coronavirus/COVID-19: Shugaban ‘yansandan Najeriya ya bukaci a rage zuwa ofishin ‘yansanda in ba dole ba sannan ‘ya sandan su rage kama mutane
Shugaban 'yansandan Najeriya,Muhammad Adamu ya bukaci 'yan Najeriya da su rage zuwa ofishin 'yansanda in ba wai abin ya zama dole ba.
Ya fitar da sanarwarne ta hannun me magana da yawun rundunar,Frank Mba inda yace suma 'yan sanda su kula da lafiyar jikinsu kan yanda ake fama da cutarnan na Coronavirus/COVID-19.
Ya bukaci 'yansandan da kansu rage kamawa da tsare mutane indai ba abinda ya shafi ta'addanci ko fashi da makami ko kisa da sauran laifikan da ba'a bayar da beli akansu ba.
Ya bukaci bincike da tantance masu laifi kamin a tsaresu.
Sanarwar ta kara da cewa, 'yansanda su ta batar su tsaida dokar hana taruwar mutane da gwamnatin tarayya ta saka a yankunan da suke aiki.
Sanna kuma a kulle makarantun horar da '...