fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Kiwon Lafiya

Italia ta rufe daukacin makarantu bayan mutuwar mutane 107 dalilin Coronavirus

Italia ta rufe daukacin makarantu bayan mutuwar mutane 107 dalilin Coronavirus

Kiwon Lafiya
Kasar Italia ta sanar da rufe makarantu da jami’oin kasar baki daya daga yau laraba har zuwa ranar 15 ga wata saboda mutuwar mutane 107 da suka kamu da cutar coronavirus.   Wannan mataki shine mafi tsauri da wata kasar Turai ta dauka sakamakon barkewar cutar bayan taron kasashen G7 masu karfin tattalin arzikin duniya.   Hukumomin Italia sun ce yau larabar mutane 28 suka mutu, wanda shine adadi mafi yawa tun bayan barkewar wadda aka tabbatar ta kama mutane sama da 3,000. Rahotanni sun ce hukumomin kasar na cigaba da nazari wajen daukar matakin gudanar da gasar kwallon kafar Serie A ba tare da ‘yan kallo ba na wata guda domin dakile yaduwar cutar.
A yi hattara: Takardun kudi da suka tsufa ka iya yada cutar Coronavirus>>WHO

A yi hattara: Takardun kudi da suka tsufa ka iya yada cutar Coronavirus>>WHO

Kiwon Lafiya
Hukumar lafiya WHO ta gargadi amfani da takaddar kudi inda tace hakan ka iya kara karfin ya duwar cutar coronavirus.  ta shawarci yin amfani da hanyoyin zamani don kauracewa yin amfani da takaddun kudi, yazama wajubi mutane sukula su tabbaba sun kiyaye a cewar hukamar. Hakazalika kungiyar ta shawarci masu hada hadar kudi, da suna wanke hannuwan su a duk sa'adda sukai ta'ammali da abokan kasuwancin su. domin cutar ka iya makalewa a jikin kudi. Shima Babban bankin Ingila yayi karin haske, inda ya tabbatar da cewa lalle takaddun kudi, sukan zama mafaka ga kwayoyin cututuka. Hakan ya biyo bayan da kasar China ta dauki matakin hana yin Amfani da takaddun Kudi, domin dakile kara yaduwar cutar, da takici taki cinyewa.
Dangote zai Kashe Milliyan 200 don yaki da cutar coronavirus a Najeriya

Dangote zai Kashe Milliyan 200 don yaki da cutar coronavirus a Najeriya

Kiwon Lafiya
Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta dauki alkawarin Naira miliyan 200 don tallafawa kokarin Gwamnatin Tarayya akan dakile yaduwar cutar Covid-19 (CoronaVirus) a kasar. Ms Zouera Youssoufou, Babbar Darakta a Gidauniyar Aliko Dangote, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata a Legas, ta ce bayar da gudummawar wani bangare ne na manufar gidauniyar.  Youssoufou ta bayyana cewa, an ware kudi kimanin  miliyan N124 don tallafawa wuraren da za su taimaka wajen dakile sake bullar cutar da kayan aiki, musamman guraran shige da fuce na kasa, A cewarta, burin gidauniyar dangote shine taimakawa gwamnati, wajan Samar da ingattaccen kiwon lafiya ga yan kasa. Akwai kuma Miliyan 36 da aka ware wajan yin aikin binciken masu dauke da cutar sannan akwai kuma miliyan 48 itama da za'a y amfan...
Coronavirus: Hukumar NCDC ta karyata killace shugabanta

Coronavirus: Hukumar NCDC ta karyata killace shugabanta

Kiwon Lafiya
Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta karyata wani rahoto da ke cewa an killace shugabanta Dakta Chikwe Ihekweazu kan cutar Coronavirus.   A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta bayyana cewa tsakanin 16 zuwa 24 ga watan Fabrairun 2020, Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta tura wata tawaga ta musamman zuwa China.   Tawagar na dauke kwararru 25 ciki kuwa har da Darakta Janar na hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya wato NCDC.   Tawagar ta tattauna da kwararru a fannin lafiya a China domin su fahimci matakan da Chinar ke dauka na shawo kan cutar COVID-19.   Hukumar ta bayyana cewa ko bayan da daraktan ya dawo daga tafiya, sai da aka yi masa gwaji aka tabbatar ba shi dauke da cutar ta COVID-19.   Cutar c...
An killace shugaban hukumar kula da cutuka ta Najeriya saboda Coronavirus

An killace shugaban hukumar kula da cutuka ta Najeriya saboda Coronavirus

Kiwon Lafiya
Ministan lafiya, Osagie Ehanire ya bayyan cewa an killace shugaban hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC, Chikwe Ihekweazu na tsawon kwanaki 14 saboda cutar Coronavirus.   Ministan ya bayyana hake a Yau, Talata a gaban kwamitin sanatoci inda ya bayyana dan gaya musu halin da ake ciki da kan matakan da hukukar ta dauka na magance yaduwar cutar.   Ya kara da cewa, an killace Ihekweazu ne bayan dawowa da yayi daga ziyarar da ya kai kasar China.   Yace matakin da aka dauka shine killace duk wani mutum da ya fito daga kasar China zuwa kasarnan na tsawon kwanaki 14 kamin ya fara mu'amala da sauran mutane kamar yanda, Vanguard ta ruwaito.
Annobar coronavirus ta bulla kasar Saudiya

Annobar coronavirus ta bulla kasar Saudiya

Kiwon Lafiya
Hukumar lafiya dake kasar saudiya ta tabbatar da lamarin inda ta bayyana bullar cutar a Karan farko a kasarta, Cutar ta bulla ne, ga wani mazaunin Saudiya a Iran, inda rahoto ya bayyana cewa, mutumin ya dawo kasar ta Saudia daga kasar Iran, bayan da aka gwada shi, aka same shi yana dauke da cutar COVD 19. a makon da ya gabata ne, hukumar kasar saudiya ta dakatar da masu ibada dake shiga kasarta, domin tabbatar da tsare lafiyar mazauna kasar daga bullar Annobar cutar coronavirus. Inda a Najeriya kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi Kira da yan kasa da su kwantar da hankalinsu, bayan da aka samu bullar cutar daga wani mazaunin kasar italiya da ya shigo Nigeria
Coronavirus: Saudiyya za ta mayar wa maniyyata aikin Umrah kudadensu

Coronavirus: Saudiyya za ta mayar wa maniyyata aikin Umrah kudadensu

Kiwon Lafiya
Ma'aikatar kula da aikin Hajji da Umrah a kasar Saudiya ta ce za ta mayar wa maniyyata aikin Umra ko ziyarar kabarin Annabi Muhammad (SAW) kudadensu.   Matakin mayar da kudaden ya zo ne bayan dakatar da aikin ibada da hukumomin kasar suka yi a matakin wucin gadi.   Fargaba kan bazuwar cutar coronavirus da ke ci gaba da yaduwa a kasashen duniya ce ta sanya kasar daukar wannan mataki.   Saudiyya na daga cikin jerin kasashe na baya bayan nan da suka tabbatar da bullar cutar Coronavirus a kasashensu.   Mutun na farko da aka samu da cutar a Saudiyya ya shigo da ita ne bayan tafiya Bahrain da Iran.   Yan kwanakin da suka wuce ne Saudiyya ta dauki matakin dakatar da yan kasashen waje shiga kasar domin gudanar da ibadar Umrah a biranen Makkah ...
Corona: Farashin man goge hannu da takunkumin rufe fuska sun tashi a Lagos

Corona: Farashin man goge hannu da takunkumin rufe fuska sun tashi a Lagos

Kiwon Lafiya
Al'ummar jihohin Lagos da Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya sun fara kokawa kan tashin farashin man goge hannu don hana kamuwa da cututtuka da kuma takunkumin rufe baki da hanci, wadanda ake rububin amfani da su saboda yaduwar coronavirus. Mutane na ta korafi cewa masu shagunan magunguna wato kemis, sun tsauwala farashin man goge hannun wanda ya tashi daga naira dubu 2,500 zuwa dubu 19,000. Wani abin da shi ma ya kara farashi shi ne na takunkumin rufe baki da hanci domin samun kariya daga harbuwa daga cutar. Wakilin BBC a Legas Umar Shehu Elleman ya jiyo ra'ayoyin mutane a game da matakan da suke dauka kan hauhawar farashin. Wani mutum ya ce: "Kalubalen da muke fuskanta a yanzu shi ne farashin man shafawa a hannu domin samun kariya daga harbuwa da cuta ya yi sama. "A ji...
Dan Najeriya ya gano maganin cutar Coronavirus data addabi Duniya

Dan Najeriya ya gano maganin cutar Coronavirus data addabi Duniya

Kiwon Lafiya
Tsohon shugaban hukumar zabe ya kasa,Maurice Iwuya bayyana cewa shi da tawagarsa sun gano maganin cutarnan data Addabi Duniya ta Coronavirus. Iwu  wanda shine shugaban hukumar binciken kimiyyar Lafiya ta kasa ya bayyana hakane ranar Litinin yayin da ya kaiwa ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu dana lafiya, Osagie Ehanire ziyara a Abuja. Da yake karin bayani kan wannan Lamari, Iwu ya bayyana cewa tun a shekarar 2015 ne hukumar tashi ta gano maganin da ka iya warkar da cutar inda ta adanashi,yanzu kuma tana neman izinin gwamnatin tarayyane dan a fara aikin samar dashi, kamar yansa Vanguard ta ruwaito. Juma'ar data gabatane Najeriya ta shaida mutum na farko dake dauke da cutar inda aka kilace mutane 20 da yayi alaka dasu.

Maza sun fi mata kamuwa da cutar Coronavirus saboda karkon garkuwar jiki

Kiwon Lafiya
Kamar yadda bayanai daga Chaina suka nunar cewa sau daya ne kwayar cutar ta yadu daga dabba zuwa dan Adam daga nan ta ci gaba da yaduwa. Sai dai sabanin kwayar cutar da ke sa mura da za a iya cewa kusan kowa ya taba harbuwa da ita akalla sau daya, amma garkuwar jikin dan Adam ba ta shirya ga wannan sabuwar kwayar cutar ba domin yanzu ne karon farko da dan Adam ya harbu da ita. A cewar wani kwararran masanin kwayoyin cututtuka Thomas Pietschmann ya yi bayani inda yace,  tsanani ko saukin cutar ya dogara ga yawan shekaru da lafiyar jiki wanda ya kamu da ita, amma jinsi na taka rawa a nan inda a dangane da Coronavirus yawan mazan da ta yi ajalinsu ya fi mata, Thomas yace  "Kasancewa wasu kwayoyin garkuwar jiki da ke gane jiki ya kamu da cuta na da alaka da kwayoyinn halitta. Kasancew...