Sunday, July 21
Shadow

Zufa

Maganin zufar fuska

Zufa
Zufar fuska abune da masu fama dashi ke ci musu tuwo a kwarya. Yawanci abinda ke kawota shine: Cin abinci me zafi. Yanayin Zafi. Damuwa ko shiga halin matsi. Razana ko Bacin rai. Motsa jiki. Abubuwan da za'a gwada dan magance matsalar zufa a fuska sune: Yin Wanka akai-akai. Aje Tawul ko Hankici dan goge zufar. Amfani da hoda marar kamshi dan tsotse zufar. A daina cin abinci me yaji ko shan Coffee. Saka kayan da basu da nauyi wanda iska na ratsasu. Shan ruwa akai-akai. Amfani da mafici ko fankar hannu.

Maganin zufar hammata

Zufa
Zufar hammata bata da dadi inda idan ta yi yawa takan sa mutum ya rika wari wanda zai dameshi, ya kuma dami mutanen dake kusa dashi. Dan hakane masu fama da zufar hammata ke neman hanyar kawar da ita. Akwai hanyoyi da yawa na kawar da zufar hammata kuma ana iya samar dasu a gida ba tare da ganin likita ba. Daya daga cikin hanyar magance matsalar zufar hamata itace a bari jiki ya bushe bayan an yi wanka kamin a saka kaya. Masana kiwon lafiya sun ce hakan na da matukar tasiri wajan magance matsalar zufar hammata. Aske Gashin Hamata: Aske Gashin hamata yana rage zufar hamatar da kuma warin da hamatar ke yi. A daina cin abinci me sanya zufa, kalar abincin da ake ci na takmakawa wajan yawan zufar da ake fama da ita. Abincin dake sanya zufa sun hada da: Abinci me yaji ...

Maganin yawan zufa

Zufa
Maganin yawan zufa (hyperhidrosis) yana iya haɗawa da sauye-sauyen rayuwa, amfani da magungunan gida, da kuma magunguna na zamani. Ga wasu hanyoyi da magunguna da za su taimaka wajen rage yawan zufa: 1. Sauye-sauyen Rayuwa Rage Tashin Hankali da Damuwa: Tashin hankali yana iya ƙara zufa, don haka yin yoga, aikin numfashi (breathing exercises), ko meditation na iya taimakawa. Guje wa Abinci Mai Dumi da Mai Yawan Yaji: Abinci mai yawan yaji yana iya ƙara zufa, don haka ana ba da shawarar guje masa. Rage Sha Barasa da Caffeine: Barasa da caffeine suna ƙara zufa, don haka yana da kyau a rage shan su. 2. Amfani da Magungunan Gida Shafa Lemon Tsami: Lemon tsami yana ɗauke da sinadaran da ke rage zufa. Ana iya shafa ruwan lemon tsami a wuraren da ake yawan zufa kafin kwanciy...