
Likitocin Uganda sun roƙi Yoweri Musaveni ya tsaya takarar shugaban ƙasar a karo na bakwai
Wasu gungun likitoci a Uganda sun haifar da cece-ku-ce bayan da suka durƙusa a gaban shugaban ƙasar Yoweri Musaveni suna roƙon sa ya tsaya takarar shugaban ƙasa a karo na bakwai.
Musaveni mai shekara 78 ya kasance kan mulki tun shekarar 1986. Sannan za a gudanar da zaɓen ƙasar na gaba ne a shekarar 2026.
Likitocin ƙarƙashin Ƙungiyar likitoci ta Uganda (UMA) suna halartar wani taro ne kan kishin ƙasa a Kampala, babban birnin ƙasar, lokacin da shugabansu ya jagorance su suka duka a gaban shugaban ƙasar domin roƙon sa.
Shafin yaɗa labaru na Nile Post ya ruwaito shugaban ƙungiyar likitocin Dr Samuel Odongo Oledo na yaba wa shugaban ƙasar, wanda ya ce ya gyara harakar kiwon lafiya tare da inganta walwalar likitoci.
Daga BBChausa.