
Jami’an tsaron Najeriya sun ‘kashe ƴan fashi huɗu’ a Kaduna
Dakarun Sojan Najeriya sun kashe 'yan fashin daji huɗu yayin wani samame da suka kai kan sansanoninsu a Jihar Kaduna.
Kwamashinan Tsaro na Kaduna Samuel Aruwan ya ce dakarun da ke cikin rundunar Operation Forest Sanity sun kashe mutanen ne a yankin Ƙaramar Hukumar Chikun.
Cikin sanarwar da ya fitar a yau Lahadi, Mista Aruwan ya ce sojoji sun bi sawun 'yan bindigar ne tare da kashe biyu daga cikinsu.
Rahotannin sirri da gwamnati ta samu daga yankin sun bayyana cewa ƙarin biyu sun mutu sakamakon raunukan da suka ji, in ji kwamashinan, yayin da rahotannin suka bayyana sunan Dogo Mallam da Bello Mallam cikin 'yan fashin da aka kashe.
Ya ƙara da cewa dakarun su ƙwace bindigar AK-47 da babur ɗaya da kuma harsasai.