
Fashi da makami aka min>>Inji Abba Gida-Gida
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-Gida ya bayyana cewa, fashi da makami aka masa a kotun daukaka kara.
Ita dai kotun ta daukaka kara ta bayyana cewa, Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC ne ya lashe zaben gwamnan jihar Kano.
Gwamna Abba yace bai yadda ba kuma zai garzaya kotu kan lamarin.