
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya Da Sace Matan Aure 10 A Katsina
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya Da Sace Matan Aure 10 A Katsina
A daren Alhamis ɗin da ta gabata, yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a kauyen Katsalle da ke gundumar Rafin Iwa ta ƙaramar hukumar Sabuwa a jihar Katsina, inda suka kashe Malam Khalid Alhaji Saleh, ɗan shekara arba'in da biyar da haihuwa da kuma sace matan aure Goma.
Majiyar RARIYA ta naƙalto cewa yan bindigar sun je garin Katsalle da misalin karfe ɗayan daren Alhamis, da shigar su suka fara harbe-harbe ba kyaf-kyaftawa, inda suka kashe mutum daya da kuma sace matan aure guda goma.
Har zuwa haɗa wannan rahotan, yan bindigar ba su tuntuɓi iyalan wadanda suka sace ba.
Allah ya kuɓutar da su cikin Aminci!