
Wata mata a Amurka ta yi kokarin bude kofar jirgin sama ana tsaka da tafiya
Wata mata ta yi kokarin tilasta wa jami’an jirgin Southwest Airlines da ya tashi daga Houston zuwa Columbus, da Ohio yin saukar gaggawa a Little Rock, Arkansas a ranar Asabar din da ta gabata, bayan da ta yi ikirarin cewa Yesu ne ya bata umarnin ta bude kofar jirgin.
Bayanan da kotun Arkansas sun ce matar mai shekaru 34 ta nufi kujerar baya a cikin jirgin, inda ta rika kallon kofar da ake amfani da ita wajen fitar gaggawa.
A cewar kotun, guda daga cikin jami’an jirgin ya shaidawa matar ko dai ta shiga bandaki idan amfani za ta yi da shi, ko kuma ta zauna.
Haka zalika, daya daga cikin ma’aikatan jirgin ya shaidawa kotun cewa, matar ta tambaye su cewa tana so a bude mata taga, amma lokacin da ta samu amsar da bata yi mat aba sai ta yi amfani da karfinta wajen kokarin bude ...