fbpx
Thursday, December 7
Shadow

labarin zamfara ayau

‘Yan sanda sun daƙile hare-haren ‘yan bindiga a Zamfara

‘Yan sanda sun daƙile hare-haren ‘yan bindiga a Zamfara

labarin zamfara ayau
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta samu nasarar daƙile hare-haren 'yan bindiga a faɗin ƙananan hukumomin jihar guda hudu, tare da kuɓutar da wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar SP Mohammed Shehu, ya fitar ya ce 'yan bindigar sun yi ƙoƙarin kai hare-hare a wasu ƙauyuka da ke ƙananan hukumomin Maru, da Bungudu, da Tsafe da kuma ƙaramar hukumar Bukkuyum. Ya ce jami'ansu sun samu nasarar daƙile hare-haren ta hanyar bayanan sirri da suka samu. SP Mohammed Shehu, ya ƙara da cewa daga ranar Juma'a zuwa Lahadi sun samu bayanan sirri da ke nuna cewa 'yan bindigar na shirin ƙaddamar da hare-hare tare da mutane a ƙauyukan da ke wanɗannan ƙananan hukumomi.
Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukucin Share Masallacin Juma’a A Garin Gusau Saboda Ya Mari Malamin Makarantar Islamiyya

Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukucin Share Masallacin Juma’a A Garin Gusau Saboda Ya Mari Malamin Makarantar Islamiyya

labarin zamfara ayau, Uncategorized
Daga Hajiya Mariya Azare Wata babbar kotun addinin islama ta yankewa wani magidanci hukuncin share masallacin Juma'a a garin Gusau dake jihar Zamfara saboda ya mari malamin lslamiya. Kotun ta yanke wannan hukuncin ne biyo bayan tuhumar mutumin da marin malamin makarantan islamiyan da yake koyar da 'yarsa. Alkalin kotun ya ce "tunda Allah ya sa kai ma musulmi ne gashi kuma gobe Juma'a to hukuncin ka shine, ka je ka share ciki da wajen wani babban masallacin Juma'a. Daga Rariya.
Dan PDP a Zamfara, Alhaji Mas’ud Danguruf ya koma APC

Dan PDP a Zamfara, Alhaji Mas’ud Danguruf ya koma APC

labarin zamfara ayau, Siyasa
Ɗan siyasa, shahararren ɗan kasuwa Alhaji Mas'ud Ɗanguruf yayi zama na musamman da ɗan takarar shugaban kasar Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Alhaji Mas'ud Ɗanguruf wanda jigo ne a jam'iyyar PDP kuma na hannun daman Atiku Abubakar da ya bada gudunmawa wajen yaƙin neman zaɓen shi a zaɓen shekarar 2019. Tun bayan ɓullar hotunan ɗanguruf da Gwamnan Zamfara Governor Bello Matawalle a farkon sati anyi ta ce-ce-kuce akan giɓin da Ɗanguruf zai bari a jam'iyyar PDP idan har ta tabbata yabar jam'iyyar kasancewar shi jigo acikin ta.
Abin Alfahari:’Yar Najariya, Khadija Haliru ta fito takarar Kansila a kasar Canada kuma ta lashe zaben

Abin Alfahari:’Yar Najariya, Khadija Haliru ta fito takarar Kansila a kasar Canada kuma ta lashe zaben

labarin zamfara ayau, Siyasa
Wannan wata 'yan Najariya ce data fito takarar Kansila a yankin Ingersoll dake Ontario na kasar Canada.   Kuma ta yi nasara.   Mina taya Khadija Mamudu-Haliru Murna. Nigerian in Diaspora. Nana Khadijah Mamudu-Haliru has done us proud.. She contested for councullorship in Ingersoll of Ontario council in far away Canada and has won..Congrats #ProudlyNigerian https://t.co/AiDAkNEf4R
Ƴan bindiga Sun buɗewa masallata Wuta Suna tsaka da Sallan Subahi a Zamfara

Ƴan bindiga Sun buɗewa masallata Wuta Suna tsaka da Sallan Subahi a Zamfara

labarin zamfara ayau
Daga Muhammad Sani Sa'eed Garba. Da Sanyin Safiyar na yau Laraba, Jaridar ALFIJIR HAUSA ke cin karo da wani rahoto. dake bayyana cewa, wasu mahara a cikin Shirin su na katta kwanane sukayi yi dirar mikiya akan wasu masallata na Subahi acikin masallaci dake cikin wani ƙauye da ake kira da Dabon Gida.” “Hakan dake cigaba ƙunshe a cikin rahoton da aka bamu, na nuni cewa, garin da lamarin ya faru wato ƙauyen Dabon Gida bai fi kilo mita ɗayaba da babban garin na Magami Maitarkoba duk a Jihar Zamfara ba.” Bugu da ƙari, maharan Sun kashe mutane Uku daga cikin masallatan a nan take Sakamakon buɗe wutan da Sukayi a cikin masallacin kan mai uwa da wabi, bisani Sun yi garkuwa da sauran masallatan.” “Wakilin namu ya tabbatar mana da faruwar lamarin, ya cigaba da cewa daga cikin waɗanda Ƴan...