
An gurfanar dashi saboda yiwa karamin yaro luwadi ta karfin tsiya a jihar Adamawa
An gurfanar da Sani Salihu dan shekaru 45 a gaban kotu a jihar Adamawa saboda yin luwadi da karamin yaro me shekaru 14.
Wanda ake zargin dai ya fito ne daga kauyen Juppa Jam na karamar hukumar Yola.
Saidai ya ki amsa laifinsa, alkalin kotun ya dage sauraren karar sai 20 ga watan Yuli inda yace a kai wanda ake zargi gidan yari.
Hakanan an yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari ko biyan tarar Naira 100 akan laifin kokarin tserewa yayin da aka kamashi.