Maganin yawan bacci
Domin magance yawan bacci, ka tsarawa kanka yanda zaka rika bacci kuma ya zama a kullun a daidai wannan lokacin kake kwanciya.
Sannan ka kiyaye, kada ka rika shan Coffee ko giya, sannan kada ka rika cin abinci me yawa sosai musamman da dare kamin ka kwanta.
Sannan ka rika motsa jiki akai-akai.
Sannan ka daina kallon TV akalla awa daya kamin ka kwanta, saboda hasken TV ko waya na iya kawo tangarda wajan yin bacci.
Idan da hali, ka yi wanka da ruwan dumi kamin ka kwanta.
Hakanan kada a sha taba kamin a kwanta.
Idan kana da kiba da yawa a yi kokarin ragewa ta hanyar azumi ko motsa jiki.
Yana da kyau kuma a rika shan ruwa akai-akai.