Mallaka da tumfafiya
Wa kike so ko kake ka mallaka, Budurwace, Saurayine? Akwai hanyoyin Mallaka da Tumfafiya da ake amfani dasu.
Saidai ba kowa ya sansu ba kuma ba kowane yakewa aiki ba sai wanda yayi dace.
Amma menene ingancin Amfani da Tumfafiya wajan mallkar wani?
Maganar gaskiya itace wannan hanya bata da inganci,zai iya zama sihiri ne ko surkulle wanda zai iya yin aiki, zai kuma iya zama bai yi aiki ba.
Ana mallaka ne ta hanyar kyautatawa da mu'amala me kyau.
Koma wanene kike so ko kake ka mallaka, babbar hanyar da za'a bi shine kyautatawa.
Muna maganar Kyautatawa ta bangaren Kyauta, kalamai, da mu'amala.
Misali Idan Mijine:
Ki rika kyautata masa ta hanyar tsaftace kanki farko, ya zamana bakinki baya wari, jikinki baya wari, kayan jikinki tsaf-tsaf masu kama jiki da fiddo surar ji...