Monday, March 30
Shadow

Nishaɗi

Dai dan wani karkataccan wani ta sanyawa yan tagwayen ta suna Corona da Virus

Dai dan wani karkataccan wani ta sanyawa yan tagwayen ta suna Corona da Virus

Nishaɗi
Matar dai mai suna Annamaria José Raphael Gonzalez, ta kamu da cutar corona ne, a asbitin da taje haihuwa bayan da tai hulda da masu dauke da cutur a wani asbiti dake kasar Mexico, La Villa General Hospital. Kamar yadda daily report ta rawaito cewa bayan matar ta haifi yan biyu, sai likitan ta ya sanar da ita cewa ta kamu da cutar Covid-19 inda ya kuma zolaye ta data sanya musu suna Corona da virus. A cewar Annamaria a lokacin da taji likitan ya ammbaci sunan tayi farin ciki matuka domin kuwa batai tunanin daman sunan da zata sawa yan tagwayan nata ba. Likitan mai suna Doctor Eduardo Castillas ya bayyana cewa "na fadi sunan ne domin zolaya ne kawai ganin yadda matar ta haifi yan tagwaye cikin koshin lafiya, amma abun mamaki sai gashi matar tai na'am da sunan dana fada". Y
Kalli abinda zaman gida yasa Ahmad Musa

Kalli abinda zaman gida yasa Ahmad Musa

Nishaɗi
Tauraron dan kwallon Najeriya dake bugawa kungiyar kwallon kafa ta Alnassr dake kasar Saudiyya, Ahmad Musa kenan a wannan hoton yake wasa a kudiddifin ninqaya.   Ya bayyana cewa, dalilin zaman gida dole(saboda Cutar Coronavirus) yasa haka.   https://www.instagram.com/p/B-RtkUsDy81/?igshid=1ekx641o1qbzz   A kasar Saudiyya ma hukumomi sun saka dokar zaman gida dan dakike yaduwar cutar Coronavirus.
Wasu sanannun mutane sai su saka cewa a zauna a gida a shafukansu na sada zumunta amma sai ka gansu a waje>>Nazir Sarkin Waka

Wasu sanannun mutane sai su saka cewa a zauna a gida a shafukansu na sada zumunta amma sai ka gansu a waje>>Nazir Sarkin Waka

Nishaɗi
Tauraron mawakin Hausa,Nazir Ahmad Sarkin Waka kenan a wannan bidiyon nasa inda yake magana kan sanannun mutanen dake sakawa a shafukansu cewa a zauna a Gida.   Yace irin wadannan sanannun mutane bayan sun saka wancan abu a shafinsu na sada zumunta kuma kawai kana kan layi sai ka hadu dasu.   https://www.instagram.com/p/B-NQvjjpB9q/?igshid=1i5lnshqu55xa     Nazir daiyayi wannan magana yana nishadi ba tare da ya bayyana da wa yake ba.
An gudanar da daurin aure da dama a daren ranar alhamis a jihar Kaduna a sakamkon dokar da gwamnatin jihar ta sanya

An gudanar da daurin aure da dama a daren ranar alhamis a jihar Kaduna a sakamkon dokar da gwamnatin jihar ta sanya

Nishaɗi
An gudanar da bikin aure da dama a daren ranar alhamis a jihar Kaduna A sakamakon dokar hana fita na sa’o’i 24 da gwamnatin jihar ta yi wanda ya fara aiki a daren ranar alhamis Jaridar daily trust ta rawaito cewa an shirya daurin auren ne tsakanin ranar Juma'a 26 gawatan Maris da kuma ranar asabar 27 ga wata, amma sakamakon dokar gwamnati sai aka daura auran a daran Alhamis, sannan kuma aka kai amaraya duka a daran Alhamis tare da yin watsi da sauran al'adun gargajiyar da Hausa Fulani suka saba yi a bukukuwan auren su. Daurin auren anyi shine dai a Kabala da unguwar shanu dake jihar Kaduna. Wata yar uwa ga amarya Aisha Ibrahim tace "an kira mune kawai ta waya inda a ka shaida mana an riga an daura aure amarya zata tafi gidan mijin ta, a sakamakon dokar da gwamnatin jihar ta s
FARGABAR CORONAVIRUS: Zaharadden Sani ya killace kansa na kwana biyu

FARGABAR CORONAVIRUS: Zaharadden Sani ya killace kansa na kwana biyu

Nishaɗi
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Kannywood ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES a Kaduna cewa fargaban gwajin jinin Ali Nuhu da aka ce za ayi kan cutar coronavirus ya dimauta shi har ya killace kansa nan da nan.     Zaharaddeen ya ce har ya dan yi wasiyyoyi ga iyalan sa cewa to ta-fa faru ta Kare, domin kila ya kamu da cutar coronavirus.     Babban dalilin fadin haka kuwa shine ya na daga cikin wadanda suka yi cudanya da Ali Nuhu a wadannan kwanaki.     ” Ali Nuhu jarumi ne a sabon fim dina da na gama dauka mai suna Haduwar Hanya.     ” Mun tafka mu’amula da cudanya matuka tare, kaga ko idan kaji irin haka dole hankalin ka ya tashi.     Zaharaddeen ya ce yana jin haka sai ya koma gida ya killace