
Ji martanin da Nafisa Abdullahi ta baiwa wani da ya ce mata ina bidiyon tsiraicin da tace zata yi?
A kwanakin bayane lokacin dambarwar bidiyon tsiraicin tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth, Abokiyar aikinta, Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa itama fa idan ta bushi iska za'a iya ganin hotunanta daga ita sai rigar mama da dan kamfai.
Waccan magana da ta yi ta dauki hankula sosai inda akai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.
Bayan saka Hotunanta a shafinta na Instagram, wani ya cewa Nafisar shin ina maganar bidiyon tsiraicin da tace zata yi?
Sai ta bashi amsar cewa da kwadayinsa zai mutu.