
Buhari ya ji ihun da aka masa a Maiduguri: Ji martanin daya mayar
Fadar shugaban Najeriya ta ce ta ji yadda wani rukunin mutane suka yi wa tawagar shugaba Buhari ihu a yayin da ya kai ziyarar jaje a Maiduguri.
Mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya ce, wanda ya dauki bidiyon da ya bazu a shafukan intanet da ke nuna ana yi wa Buhari ihu bai a yi wa mutanen Borno adalci ba wadanda ya ce an san su da karamci da son baki.
"Da ni aka shiga gari tun daga filin jirgin sama zuwa fadar Shehu kuma jama'a ne suka fito suna cewa sun gode suna ala san barka."
"Amma akwai wata matattara da suke cewa ba sa so, kuma ni ma na ji da kai na masu cewa ba sa so," in ji Garba Shehu.
Buhari dai ya ziyarci Maiduguri ne domin jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar bisa harin Auno da Boko Haram ta kai kan wasu matafiya abin da ya yi sanadiyyar mutuwar...