fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Nishaɗi

Chelsea na daf da sayen Hakim Ziyech daga Ajax

Chelsea na daf da sayen Hakim Ziyech daga Ajax

Nishaɗi, Uncategorized
Tattaunawa ta yi nisa tsakanin Chelsea da Ajax kan sayen dan wasan gaba Hakim Ziyech a wannan kaka kan kudi fam miliyan 38, kuma nan ba da dadewa ba zaa sanar da kammaluwar cinikin. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); A watan Janairu Chelsea ta so sayen dan wasan mai shekaru 26, amma kungiyar Ajax ta nuna ba za ta sayar ba saboda kokarin da take na lashe gasar kasar Holland. Sayen dan wasan dan kasar Morocco da Chelsea za ta yi, zai kasance na farko tun bayan haramcin da aka wa kungiyar na sayen sabbin ‘yan wasa. An sha rade radin cewa Chelsea za ta sayi wasu ‘yan wasa a lokacin da aka bude kasuwar hada – hadar ‘yan wasa ta watan Janairu cikin su har da dan wasan gaba na Paris Saint Germain Edinson Cavani da na Napoli Dries Mertens. Ziyech ya bada gudummawa...
Buhari ya ji ihun da aka masa a Maiduguri: Ji martanin daya mayar

Buhari ya ji ihun da aka masa a Maiduguri: Ji martanin daya mayar

Nishaɗi, Uncategorized
Fadar shugaban Najeriya ta ce ta ji yadda wani rukunin mutane suka yi wa tawagar shugaba Buhari ihu a yayin da ya kai ziyarar jaje a Maiduguri. Mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya ce, wanda ya dauki bidiyon da ya bazu a shafukan intanet da ke nuna ana yi wa Buhari ihu bai a yi wa mutanen Borno adalci ba wadanda ya ce an san su da karamci da son baki. "Da ni aka shiga gari tun daga filin jirgin sama zuwa fadar Shehu kuma jama'a ne suka fito suna cewa sun gode suna ala san barka." "Amma akwai wata matattara da suke cewa ba sa so, kuma ni ma na ji da kai na masu cewa ba sa so," in ji Garba Shehu. Buhari dai ya ziyarci Maiduguri ne domin jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar bisa harin Auno da Boko Haram ta kai kan wasu matafiya abin da ya yi sanadiyyar mutuwar...
RAHOTON MUSAMMAN: An fallasa yadda Diya, Aziza da Magashi suka tafka satar bilyoyin nairori

RAHOTON MUSAMMAN: An fallasa yadda Diya, Aziza da Magashi suka tafka satar bilyoyin nairori

Nishaɗi, Uncategorized
Rahotannin musamman sun bayyana yadda wasu manyan sojoji a lokacin mulkin marigayi Sani Abacha, suka bi sahun sa wajen jidar bilyoyin kudaden al’umma su na maidawa na su. Daya daga cikin wadancan manyan sojoji da a yanzu Minista ne a gwamnatin Buhari, wato Bashir Magashi, sun rika jidar kudaden su na kimshewa a kasashen waje ta hanyar tsarin bankin kasa da kasa, a wata harkalla irin ta ‘Da’u fataken dare. An rika boye kudaden a kasashen waje daga cikin kudaden danyen mai da aka rika kwasa a boye, bisa sa hannun Abacha, shugaban da Kungiyar (Transparency International) ta bayyana cewa ba taba yin rikakkun barayin shugabanni ba, kamar shi da Suharto na Indonesia da kuma Mobuto Sese-seko na Zaire, wadda a yanzu ake kira Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo. An kiyasta cewa Abacha ...