Sunday, June 7
Shadow

Nishaɗi

Hoton da Deezell ya saka tare da abokanshi ya dagawa wata matashiya hankali har tace tana son daya daga ciki

Hoton da Deezell ya saka tare da abokanshi ya dagawa wata matashiya hankali har tace tana son daya daga ciki

Nishaɗi
Tauraron mawaki,Ibrahim Rufai da aka fi sani da Deezell ya saka hoton aurensa tare da wasu abokanshi da suka haskaka.   Masoyanshi da dama sun yaba da hoton.   Saidai an samu wata data kasa Hadiye maitarta inda tace wanda bai saka babbar riga ba a cikinsu idan bai da mata a gaya masa zata cika masa addininshi.   https://twitter.com/haauwar/status/1236581167442378752?s=19    

Gwanin Ban tausai: Yanda Budurwarsa ta shekaru 3 ta gayamai su daina soyayya dan kuwa ta samu sabon masoyi

Nishaɗi
Allah Sarki Soyayya da dadi amma Rabuwa da ciwo, Kuma masu iya magana na cewa son maso wani koshin wahala.   Wani matashi da budurwarsa da yake tsananin so ta ce masa ta samu wani saurayi kuma tana so su dena soyayya su zama abokai kawai ya kasa rike abin a Ransa inda ya fito shafinsa na zada zumuntar Twitter ya zayyana yanda Abin ya faru.   Akwai wani abu da zai faru da kai idan ba ka baiwa wani Labari ba, ba za ka ji saukin Lamarin ba, watakila irin hakane tasa wannan matashi ya kasa rike abin a Zuciyarsa.   Yace sun kwashe shekaru 3 suna soyayya da wannan budurwa tasa inda a Kaduna ya Hadu da ita kumama Sanadiyyarta ya koma Kaduna da zama.   Yace tun da ta shiga jami'a ya fara ganin canji inda ta fara gaya masa cewa su rabu. Yace daga baya ta ...
Sabuwar wakar Deezell ta Crush

Sabuwar wakar Deezell ta Crush

Nishaɗi
Tauraron mawaki, Ibrahim Rufai da aka fi sani da Deezell ya saki sabuwar waka me taken Crush wadda suka yi shi da abokin aikinsa,DJ Abba.   Ya saki wakar a shafukansa na sada zumunta inda kuma tuni masoyansa suka fara yabawa da wakar.   Gurin da ya fi daukar hankali a wakar shine inda Deezell ke cewa" Bani da kati amma wait bari in ci bashi"   https://twitter.com/officialdeezell/status/1235675941906436096?s=19  
Dalilin da ya sa na maka Deezell a Kotu>>Maryam Booth

Dalilin da ya sa na maka Deezell a Kotu>>Maryam Booth

Nishaɗi
Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Hausa, Maryam Booth, ta bayyana cewa bayan shawara da da ta yi da lauyoyin, ya zama dole ta maka Deezell a kotu.   Idan ba a manta ba, a makwannin da suka gabata aka saki wani bidiyon tsaraici na dake nuna jarymar tsirara a dakin Otel tana canja kaya.   Tun a wancan lokaci mutane da dama suka rika yin tir da wannan abu da suka ga wanda ya sami wannan bidiyon tsiraici na jarumar.   Ibrahim Rufai da aka fi sani da suna Deezell ne jarumar ta zarga cewa shine yake tare da ita a wannan daki kuma shine ya dauke da wayarsa.   Daga baya ya ce ba shi bane ya yada Bidiyon sannan kuma ya shigar da kara kotu bisa zargin kazafi da aka yi masa.   Bayan haka ne Maryam ta shifar da nata karar ta neman kotu ta tilata wa
Sa’adiya Kabala ta yi Aure: Kalli hotonta da Angonta

Sa’adiya Kabala ta yi Aure: Kalli hotonta da Angonta

Nishaɗi
Ga dukkan Alamu tauraruwar fina-finan Hausa,Sa'adiya Kabala ta yi Sabon aure bada jimawaba, kamar yanda Shafin hutudole ya fahimta.   Daya daga cikin abokan aikin Sa'adiya, Aishatulhumaira ce ta bayyana haka a shafinta na sada zumuntar dandalin Instagram inda ta saka hoton Sa'adiya da Angon nata tana musu fatan Alheri inda tace Allah yasa Mutu ka raba. https://www.instagram.com/p/B9d2P-fnnyd/?igshid=1o61qqohjx5yv Itama dai Sa'adiyar a wani bidiyo data saki a shafin nata na dandalin Instagram wanda bai dade ba ta tabbatar da wannan labari inda take addu'ar Allah ya aurar dasu sannan aka ji wata Murya a baya tana fada mata cewa Ai an kusa. https://www.instagram.com/p/B9cjGRPBFEN/?igshid=jbvdz4atbbql Muna taya Sa'adiya Kabala murna da fatan Allah ya bada zaman Lafiya.
Kazafin Da Aka Yi Min Na Mu’amàla Da Matar Aure, Na Dauke Shi A Matsayin Jarabta Daga Allah, Cewar Hamisu Breaker

Kazafin Da Aka Yi Min Na Mu’amàla Da Matar Aure, Na Dauke Shi A Matsayin Jarabta Daga Allah, Cewar Hamisu Breaker

Nishaɗi
Shahararren mawakin finafinan Hausa, Hamisu Sa'idu Yusuf wanda aka fi sani da Hamisu Breaker ya bayyana cewa batun da aka danganta shi da shi na cewa ya yaudari wata matar aure zuwa masana'antar finafinan Hausa ya dauki lamarin a matsayin kazafi kuma jarabta daga Allah. Kuma yana fatan Allah ya sa ya ci wannan jarabawar.   Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata wani mawaki mai suna Aliliyo Mai Waka ya zargi Hamisu Breaker da laifin yaudaro wata matar takwaransa mawaki Adam Fasaha zuwa cikin harkar fim.   An yi zargin cewa tun kafin jarumar mai suna Momee Gombe ta fito daga gidan mijinta mawaki Breaker yake hure mata kunne, wanda kuma bayan fitowar ta din ne aka soma ganin yana saka ta a bidiyon wakokinsa, wanda hakan ya sa aka sake tabbatar da zargin da ake yi masa....