Wednesday, July 24
Shadow

Rage Tumbi

Rage kiba cikin sati daya

Rage Tumbi
Tabbas zaku iya rage kiba cikin sati daya amma abu mafi kyawu shine a shimfida tsari na rage kiba na lokaci me tsawo da yafi sati daya, kalla wata daya, biyu ko uku. Dalili kuwa shine likitoci sun ce rage kiba a sati daya na iya zamarwa mutum matsala musamman idan yana da wasu manyan ciwuka irin su hawan jini, ciwon suga, ciwon zuciya da sauransu. Sannan rage kiba a sati daya zai zama ba kitse bane kadai mutum zai rage hadda ruwan jiki da yawan naman jikin mutum wanda hakan ba zai dade ba mutum zai iya komawa yana da kiba. Amma idan aka bi abun a hakanli, za'a fi samun sakamako me gamsarwa. Saidai duk da haka,ga masu so, ga yanda za'a iya rage kiba cikin sati daya. A daina cin abincin da aka sarrafa a kamfani, irin su cakulan, kifin gwangwani, waken gwangwani, yegot, Yoghur...

Abincin dake rage kiba

Rage Tumbi
Kuna son rage kiba ta hanyar cin abinci? Ga abincin dake rage kiba kamar haka: Kwai Cin Kwai ta hanyar dafawa ko soyawa a yi Scramble Egg yana taimakawa wajan rage kiba, kuma ba sai an ci da yawa ba. Yana da sinadaran Kalori wanda basu da yawa amma kuma yana da sinadaran protein da sauransu dake taimakawa daidaita girman jiki. Gyada, Aya, Gujiya: Cin Aya, Gyada, Gujiya da danginsu yana taimakawa sosai wajan rage kiba. Suna da sinadarai masu daidaita girman jiki da kuma sawa mutum ya rage kiba wanda basu da illa. Ganye Cin ganye irin su zogale, Tafasa, Yadiya, Kabeji, latas,lansir da sauransi na taimakawa matuka wajan rage kiba. Suna da sinadaran rage kiba wanda basu da illa ga lafiya. Kifi Kamar dai kwai, Shima kifi yana bayar da sinadaran protein da fats wan...

Rage kiba cikin gaggawa

Rage Tumbi
Ana iya rage kiba cikin sauri ta hanyar amfani da wadannan hanyoyi: Yin Azumi Yin Azumi na daya daga cikin manyan hanyoyin rage kiba sosai, ko kun tuna yanda mutane ke ramewa da azumin watan Ramadana? To idan mutum na son ramewa ko rage kiba cikin gaggawa, to yayi azumi,ana iya yin Azumin Litinin da Alhamis dan samun sakamako me kyau. Daina shan Zaki Idan ana son rage Kiba cikin gaggawa a daina ko a rage shan zaki, watau zaki irinsu lemun kwalba, Yegot/Yoghurt da sauransu. Ana iya rika amfani da zuma, Mazarkwaila, rake da sauran hanyoyin samun zagi wanda ba na bature ba ko suma ayi amfani dasu saisa-saisa. A rage Amfani da kayan da bature ya sarrafa: A rage cin kayan da aka sarrafa na roba, leda, da kwalba, a yawaita amfani da kayan da aka hada a gida maimakon na k...

Rage tumbi da zogale

Rage Tumbi
Zogale na da amfani da yawa, rage Tumbi da kiba na daya daga cikin manyan Amfanin Zogale. A wani bincike da masana suka gudanar akan mutane 41, an rika basu wani hadin kurkur, Zogale da Curry na tsawon sati 8 inda suka rika hadawa da motsa jiki. Hakan ya taimaka musu sun rage kiba sosai. Hodar Zogale: Hakanan bincike ya tabbatar da cewa,hodar ganyen zogale na taimakawa wajan rage kiba, ana iya barbadata kamar yaji ko gishiri a cikin abincin da za'a ci. Shagin Zogale: Ana iya hada shayin Zogale da Coffee a rika sha wanda shima yana taimakawa wajan rage kiba. Domin samun amfanin sosai, ana iya fara shan shayin zogale kamin a ci komai da safe. Ana kuma samun ganyen zogale a wanke. A zuba a blender a zuba ruwa a markada, idan ba' da blender a yi amfani da Turmi a daka ana...

Maganin rage tumbi

Rage Tumbi
Maganin rage kiba wanda bashi da illa a hankali ake samun sa, mafi yawan abubuwan rage kiba na dare daya suna illa sosai. Ga hanyoyin da ake bu wajan rage kiba ba tare da shan magani ba: A rage cin kayan zaki wanda basu da fiber. A rage shan lemun kwalba, Biredi, cincin,biskit da sauransu, a yawaita cin Wake, Alkama, kwai, kifi da nama wanda bashi da illa. A Motsa jiki: Motsa jiki na da matukar muhimmanci idan ana son rage kiba. Ba wai sai mutum yayi abinda zai kure kansa ba, ko da tafiya da sauri-sauri ta isa, ana iya yinta na tsawon mintuna 30 zuwa 60 a kullun dan samun sakamako me kyau. A daina cin abubuwan da kamfani ya sarrafa irin na leda kwalba da roba. Anan ana maganar irinsu madarar gwagwani,Waken Gwangwani, Alewa, Biskit, da sauran duk wasu abubuwan da ba'a ...