Me ake nufi da kwaila
Kwaila na Nufin mace sabuwar Balaga amma wadda bata gama mallakar hankalin kanta ba.
Kwailanci na farawa ne daga shekaru 15 har zuwa 18 ko 19.
A tsakanin wadannan shekaru kwaila bata iya magana ba, ko saurayi ta yi, saidai yayi hakuri da ita yayi ta dorata a hanya har ta zama ta fahimci rayuwa. Duk da dai akwai kwailaye da basu da yawa masu hankali.
Hakanan a tsakanin wadannan shekaru, Kwaila na da kaguwa akan abubuwa, musamman ma soyayya, takan bayar da zuciyarta gaba daya idan ta samu saurayi me sonta.
To shiyasa a daidai wannan lokaci idan aka samu mara Imani ya gudu ya barta, zata ji kamar ta yi hauka, zata yi kunci sosai da kuka me tsanani.
Yawanci kwaila bata damu da kudi ba, ko nawa ka bata zata gode maka, abinda ta fi damuwa dashi shine, wannan kulawar da kake bata d...