
Gwamnatin jihar Legas ta jaddadawa ‘yan okada cewa har yanzu dokar hana tukin babur na nan daram
Gwamnatin jihar Legas ta jaddadawa 'yan okada cewa har yanzu dokar hana tukin babur na nan daram.
Hadimin gwamnan jihar, Hon Sola Giwa ne ya bayyyana hakan a ranar litinin, kuma yayi kira ga mutane su cigaba da dokar gwamnatin.
Kananun hukumomi goma aka haramtawa tukin baburan, wanda suka hada da Kosofe, Oshodi-Isolo, Somolu, Mushin, Apapa, Ikeja, Lagos Island, Lagos Mainland, Surulere da kuma Eti-Osa.