fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Siyasa

Nasan ku jajirtattu ne ku riga kora ‘yan bindiga idan sun kawo maku farmaki, Gwamnan jihar Ondo ya fadaw ‘yan jiharsa

Nasan ku jajirtattu ne ku riga kora ‘yan bindiga idan sun kawo maku farmaki, Gwamnan jihar Ondo ya fadaw ‘yan jiharsa

Siyasa, Tsaro
Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu yayi kira ga al'ummar jiharsa cewa su daina tsoron 'yan bindiga. Yace su riga jajircewa suna kora su cikin daji ba wai su rika guduwa cikin gidajensu ba idan sun kawo masu hari. Sannan yace koma basu kawo masu su riga farautarsu domin shi ya san 'yan jiharsa jajirtattu ne. A karshe yace abokinsa gwamnan jihar Zamfara watau Bello Matawalle fushi ne yasa shi har ya cewa mutane au sayi bindugu.
Oshiomole yace dole Atiku ya fadi kuma Tinubu yayi nasara a zaben shekarar 2023

Oshiomole yace dole Atiku ya fadi kuma Tinubu yayi nasara a zaben shekarar 2023

Breaking News, Siyasa
Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oahiomole ya bayyan dalilin dayasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu zai maye gurbin Buhari a shekarar 2023. Tsohon gwamnan jihar Edon ya kara da cewa a jihar Osun ma Oyetole zai yi nasara a ranar 16 ga watan Yuli a zaben gwamnoni. Oshiomole, wanda ke neman takarar sanata a jihar Edo yace tabbas Atiku zai fadi domin sun bata siyasar su. Amma Tinubu ne zai yi nasara ya lashe zabe kuma ya doke Atiku ya maye gurbin Buhati a Villa.
An shawarci Peter Obi cewa ya fasa yin maja da Kwankwaso

An shawarci Peter Obi cewa ya fasa yin maja da Kwankwaso

Siyasa
Kungiyar masoyan Peter Obi ta bukaci dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour Party cewa ya fasa yin maja da jam'iyyar Kwankwaso ta NNPP. Kungiyar sun bukaci ayi hakan ne bayan da suka fahimci cewa Rabi'u Kwankwaso ba zai taba janyewa Obi ba. Mai magan da yawun kungiyar masoyan, Onwuasoanya Jones ne ya bayyan hakan cewa Obi ya gaggauta daina tattaunwa akan yin maja da NNPP.
Yanzu yanzu dan takarar gwamnan jihar Kaduna, Uba sani ya bayyaba abokiyar takatarar shi

Yanzu yanzu dan takarar gwamnan jihar Kaduna, Uba sani ya bayyaba abokiyar takatarar shi

Breaking News, Siyasa
Dan takarar gwamna a jihar Kaduna, Sanata U a Sani ya zabi mataimakiyar gwamna El Rufa'i, Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takarar shi. Ya bayyana hakan ne a daren ranar litinin bayan ya gudanar da taro da manyan jam'iyyar ta APC ba Kaduna. Kuma ya kara da cewa ya zabe tane saboda gudunmawar data ke yiwa gwamna jihar Malam Nasiru.
‘Yan ta’adda sun kaiwa ‘yan mahalissar jihar Baushi hari sun ji masu rauni tare da bata masu kadarori su yayin da suke gudanar da taro

‘Yan ta’adda sun kaiwa ‘yan mahalissar jihar Baushi hari sun ji masu rauni tare da bata masu kadarori su yayin da suke gudanar da taro

Breaking News, Siyasa, Tsaro
'Yan ta'adda sun kaiwa 'yan majalissar jihar Bauchi mummunan hari a gidan suke karbar baki yayin da suke gudanar da taro. Inda suka fasa masu gilasan motoci da kuma tagogin gidan nasu, kuma sun kai harin ne kwana daya bayan da sukayi kokarin babbake gidan majalissar jihar. 'Yan ta'addan su hamsin ne suka masu wannan harin kuma sun jiwa wasu daga cikin 'yan majalissar rauni. Daya daga cikin 'yan majalissae ne ya bayyanawa manema labarai hakan, wato Ado Wakili kuma yace sun ji masa rauni shima.
Karyane bama muzgunawa Kiristoci a Najeriya>>Gwamnatin Tarayya

Karyane bama muzgunawa Kiristoci a Najeriya>>Gwamnatin Tarayya

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta yi Allah wadai da kiran da wasu sanatocin kasar Amurka suka yi na sake saka Najariya a cikin kasashen dake muzgunawa Kiristoci.   Sanatocin sun aikewa shugaban kasar ta Amurka da bukatar inda suke zargin cewa wai ba'a barin kiristoci na yin addininsu yanda ya kamata a Najeriya.   Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa, wannan magana an yi tane akan karya da kuma rashin fahimtar abinda ke faruwa a Najeriya.   Kamfanin dillancin labaran Najariya, NAN, ya ruwaito Lai Muhammad yana kasar Ingila ne dan ganawa kafafen sadarwa na kasa da kasa da kuma sauran kungiyoyi masu zaman kansu.
Shin wai da gaske Sanatocin da gwamnatin tarayya ta tura kasar Ingila su Taimakawa Ike Ekweremadu an kamasu?

Shin wai da gaske Sanatocin da gwamnatin tarayya ta tura kasar Ingila su Taimakawa Ike Ekweremadu an kamasu?

Siyasa
Rahotanni sun yadu cewa, sanatocin da majalisa ta tura kasar Ingila su taimakawa Ike Ekweremadu an kamasu.   Rahoton yace an kama sanatocinne bisa zargin alaka da Boko Haram.   Saisai zuwa yanzu wadanna  rahotanni ne kawai na shafukan sada zumunta.   A iya binciken kafar Hutudole.com, babu wata kafar yada labarai ta gwamnati ko me zaman kanta data tabbatar da wannan labari.   An dai kama Ekweremadu ne saboda zargin cirewa wani yari wani sassan jikinsa dan a dasawa diyarsa.
2023: Masu cewa a zabi musulmi shugaban kasa, mataimakinsa ma musulmi basu wa Najariya fatan Alheri>>Inji sheikh Halliru Maraya

2023: Masu cewa a zabi musulmi shugaban kasa, mataimakinsa ma musulmi basu wa Najariya fatan Alheri>>Inji sheikh Halliru Maraya

Siyasa
Tsohon hadimin gwamman jihar Kaduna kuma malamin addinin Islama, Sheikh Halliru Maraya ya bayyana cewa, masu neman a tsayar da duka 'yan takarar shugaban kasa Musulmai ko kirista basawa Najariya fatan Alheri.   Ya bayyana hakane a hirarsa da manema labarai.   Yace babu addinin da ya fi wani addini masu kwarewa da ya kamata su yi mulki idandai za'a bi cancantane.   Yace kuma masu neman a yi wannan abu ya kamata su lura da yanda a yanzu kawunan 'yan Najariya ya rabu sosai wanda hakan zai kara kawo rarrabuwar kawunan ne.
Dandazon Mata Sun Yi Bikin Kona Tsintsiyar Jam’iyyar APC A Kaduna

Dandazon Mata Sun Yi Bikin Kona Tsintsiyar Jam’iyyar APC A Kaduna

Siyasa
Dandazon Mata Sun Yi Bikin Kona Tsintsiyar Jam'iyyar APC A Kaduna Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa) Shugaban Jam'iyyar PDP na karamar hukumar Birnin Gwari da ke a jahar Kaduna Alhaji Yarima Mai Taki shi ya jagoranci kona tsintsiyar a lokacin da ya amsa wasu daga cikin matan Jam'iyyar APC zuwa Jam'iyyar PDP a jiya Lahadi. Bayan haka Jam'iyyar PDP ta gudanar da bikin kona tsintsiyar.