Saturday, June 6
Shadow

Siyasa

INEC zata kara yawan runfunan zabe

Siyasa
Hukumar zabe me zaman kanta ta kasa(INEC) ta bayyana cewa zata bude karin rumfunan zabe kamin babban zaben 2023 me zuwa.   Jami'in hukumar a jihar Kwara, Attahiru Garba Madami ne ya bayyanawa manema labarai da wannan a yayin ganawar da yayi dasu a karamar hukumar Patigi dake jihar.   Yace sun jima suna tattauna wannan batu kuma zasu yi hakanne dan kara kai rumfunan zaben kusa da jama'a
Ganduje ne ya bukaci na karbi Sarki Sanusi na II>>Gwamnan Nasarawa

Ganduje ne ya bukaci na karbi Sarki Sanusi na II>>Gwamnan Nasarawa

Siyasa
Gwamnan jihar Nasarawa da ke Najeriya, Abdullahi Sule, ya ce takwaransa na jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya kira shi a wayar tarho inda ya bukaci ya amince a kai tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II can idan an sauke shi daga kan mulki.   Ranar Litinin din makon jiya ne gwamnatin Kano ta sauke sarkin daga gadon sarauta bayan ta zarge shi da laifin kin yi wa Gwamna Ganduje biyayya. A ranar ce kuma aka dauke shi a jirgin mai saukar unguwa zuwa kauyen Loko da ke jihar Nasarawa inda ya kwana daya, ko da yake washe gari an mayar da shi garin Awe na jihar ta Nasarawa. Jaridar Daily Trust ta ambato Gwamna Sule yana shaida wa wasu 'yan jarida cewa: "Jim kadan bayan an sauke shi [Sanusi na II], gwamnan Kano ya kira ni inda ya ce 'yanzu muka sauke Sarki kuma muna
Jam’iyyar APC a jihar jigawa ta sake lashe zaben da akai

Jam’iyyar APC a jihar jigawa ta sake lashe zaben da akai

Siyasa
Dan takarar All Progressives Congress (APC), Musa Muhammad Fagen-Gawo na mazabar Bubara / Garki, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Asabar da ta gabata a jihar Jigawa. An yi wannan sanarwar ne da safiyar Lahadi a cibiyar tattara sakamakon zabe dake karamar hukumar ta Bubara ta hannun jami’in zabe mai suna Ahmad Kaugama. Jami’in ya bayyana cewa Mista Fagen-Gawo na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 48,318 hakan ya bashi damar kayar da babban abokin hamayyarsa, Nasiru Dantiye na jam’iyyar Democratic Party (PDP), wanda ya samu kuri’u 24,135. Hakanan a zaben, Bashir Umar na Action Democratic Party (ADP) ya zo na uku da kuri'u 458. Wanda ya samu nasara, Musa Fagen-Gawo na jam'iyyar APC, ya kasance da ne ga dan majalisa mai rasuwa, Muhammad Adamu-Gawo, wanda ya mutu kwana
Komawa ga Allah shine mafita a gare mu>>sakon Trump

Komawa ga Allah shine mafita a gare mu>>sakon Trump

Siyasa
Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi kira ga ‘yan kasan su koma ga Allah, kowa ya daga hannu ya roki Allah musamman a yau ranar Lahadi da ranar Ibada ne.   “Da ya ke mu Amurkawa a tsawon tarihi mukan yi tawassuli ga Ubangiji, a duk lokacin da mu ka samu kan mu cikin irin wannan mawuyacin halin, ina mai sanar da cewa ranar Lahadi 15 Ga Maris ta kasance Ranar Addu’ar Kasa Baki Daya. Za mu yi addu’o’in ne domin neman tsari da kariya daga Ubangiji.”   “A kowane hali ko yanayi ka tsinci kan ka, ina kira da ka maida himma wajen dukufa da yin addu’a tare da mika wuya da imani ga Ubangiji. Idan muka hada hannu, sai mu tsira tare sannan mu kubuta daga wannan annoba.”    
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya nuna goyon bayansa kan sauke Sarkin kano, M. Sanusi II

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya nuna goyon bayansa kan sauke Sarkin kano, M. Sanusi II

Siyasa
Shehin malamin addinin Islama,Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana goyon bayansa ga sauke Sarki Muhammad Sanusi II daga Sarkin Kano.   A cikin wani bidiyo da Hadimin gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai ya watsa a shafinsa na sada zumunta anji Malam yana bayanin cewa ya samu Kwankwaso da Gwamna Ganduje kan maganar Sarkin Kano.   https://www.facebook.com/Dawisu2016/videos/231566664651490/
Duk yanda kuka ga Sarkin Kano na jawo Aya da Hadisi ba da gaske yake ba>>Majasiddin Sarkon Kano

Duk yanda kuka ga Sarkin Kano na jawo Aya da Hadisi ba da gaske yake ba>>Majasiddin Sarkon Kano

Siyasa
Alhaji Auwalu Idi, Maja Siddin Sarkin Kano ya bayyana a wani faifan bidiyo dake ta yawo a shafukan sada zumunta inda aka jiyoshi yana ta Rantsuwa akan cewa duk abinda sarkin Kano ke fada ba gaskiya bane.   Saidai Alhaji Auwalu bai kama suna ba amma wasu masu sharhi na kyautata zaton cewa da tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yake.   Ya kara da cewa duk ayoyin Qur'ani da Sarkin ke jawowa ba da gaske yake ba.   Kalli bidiyonshi a kasa:   https://twitter.com/elmahdeey/status/1239139127137894400?s=19
Bamu san iya yawan kudin da Abacha ya sata ba>>Gwamnatin Tarayya

Bamu san iya yawan kudin da Abacha ya sata ba>>Gwamnatin Tarayya

Siyasa
Me baiwa shugaban kasa shawara kan shari'a kuma ministan shari'a na kasa,Abubakr Malami ya bayyana cewa bai san iya yawan kudin da tsohon shugaban kasa, Marigayi janar Sani Abacha ya sata ba.   Ya bayyana hakane a cikin wata wasika da ya mayarwa kungiyar kula da yanda ake gudanar da harkokin gwamnati ta SERAP data aika ma ofishinsa inda take neman bayani kan yawan kudin da Abacha ya sata da kuma abinda aka yi da kudin da aka kwato zuwa yanzu.   Malami yace daga hekarar 1999 zuwa 2015 an kwato Dala Biliya  5 na Abacha amma babu bayanin yanda aka yi amfani dasu.   Yace saidai wannan gwamnatin ta kwato Dala Miliyan 322 daga kasar Switzerland wanda kuma aka yi amfani dasu wajan shirye-shiryen inganta rayuwar 'yan kasa da rage musu radadin talauci. Yace akwai ku
Kwadayin takarar 2023 na wa jam’iyyar APC illa irin ta Coronavirus/COVID-19 >>Tinubu

Kwadayin takarar 2023 na wa jam’iyyar APC illa irin ta Coronavirus/COVID-19 >>Tinubu

Siyasa
Jigo a jam'iyya me mulkita APC, Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmad Tinubu ya nuna damuwa kan yanda wasu 'yan jam'iyyar tasu tun yanzu idanunsu sun rufe kan neman takarar shekarar 2023.   Tinubu yace a yayin da Najeriya ta ke kula da Cutar Coronavirus/COVID-19 yanda ya kamata to akwai wata cutar dake damun 'yan siyasa shine hangen 2023.   Tinubu yakara da cewa tun kamin shugaba Buhari ya shekara akan mulki su wadannan 'yan siyasa sun wasa wukakensu zasu yi yanka.   Yace Shugaban kasa, Muhamadu Buharine mutum na farko da wannan lamari yake shafa inda yace maimakon wadannan 'Yan siyasa su taimakawa shugaban ya cika Alkawuran da ya dauka amma inda suka nufa daban.   Ya bayyan cewa wadannan mutanene suka yi kutin-kutin aka dakatar da shugaban jam'...