A yau, Alhamis, Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban jam'iyyar APC,Adams Oshiomhole da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi a fadarsa ta Villa dake babban birnin tarayya, Abuja.
Ganawar tasu ta kasance a Sirri.
Kalli hotunan ganawar tasu anan
Mutane 4 masu yiwa kasa hidma NYSC na 2019 da aka tura Bauchi ne suka rasa ransu a cewar Jami'in hulda da jama'a na shirin. Sun mutu ne a yayin aikin shekara daya, na wajubi na kasa, sannan mambobin kungiyar 14 ne za su maimaita hidamar aikin.
a cewar Jami'in hulda da jama'a na shirin Namadi Abubakar wanda ya bayyana haka a ranar Alhamis a yayin wucewa ga jerin gwano na shekara, Inda ya bayyana cewa mamatan sun mutu ne sakamakon kamuwa da cututtuka sannan daya ya mutun a Sa kamakon hatsarin mota.
Ya ce daga cikin mambobi guda 14 da suka yi kuskure, bakwai an kara aikinsu zuwa watanni hudu saboda laifuffuka daban-daban kuma sauran mambobi bakwai daga ciki an ba su sanarwar sake aikin nasu.
Abubakar ya lura cewa, takunkumin da aka sanya ga membobin kung...
A ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta amince da rancen dala biliyan 22.7 wanda Shugaba Buhari ya nema bayan wata muhawara mai zafi wacce majalisar tayi bayan rufe kofa da yan' majalisun sukai wanda ya dauki tsawan mintuna 45 daga bisani kwamitin ya amince da kudirin abubuwa biyu lamunin gida dana waje, wanda Clifford Ordia ya ke Jagoranta.
Sanatocin sun hada kai kan batun tun farko game da takaddama wanda ya haifar da taron rufe kofar gaggawa, matakin da Sanata Gabriel Suswam ya ba da shawara.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ba da tabbacin cewa za a karkatar da rancen ne ga ayyukan da za su amfani rayuwar ‘yan Najeriya.
Ya kuma kalubalanci kwamitocin daban-daban na Majalisar Dattawa da su tabbatar da bin komai cikin kulawa.
...
Kamar yadda Kafar Hutudole ta rawaito akan batun Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake da zama a babban birnin tarayya,Abuja kan batun dakatar da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole daga Mukaminsa.
Inda Maishari’a, Dalami Senchine ya bayyana haka, a ranar Laraba inda ya bukaci Oshiomhole ya sauka daga mukamin nasa har sai an kammala shari’ar dake neman a saukeshi gaba daya.
Tun bayan faruwar wannan hukunci, rahotanni suke bayyana Jam'iyar APC na shirin taron NEC don maye gurbin Oshiomhole.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa wasu gwamnonin APC sun kara matsa kaimi don sanya wanda zai maye gurbin Oshiomhole a taron da gwamnonin jam'iyar za su zauna.
Wani jigo a jam’iyyar, wanda ya yi magana kan batun , ya ce, “Gwamnonin na shirin yin ki...
Shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Adams Oshiomhole ya daukaka kara bayan hukuncin wata kotu da ya sauke shi daga mukaminsa a ranar Laraba.
Mai magana da yawun shugaban Simon Ebegbulem ne ya bayyana hakan, inda ya ce sun nemi kotu ta dakatar da aiwatar da hukuncin.
"Kasancewar batun a gaban kotun daukaka kara, har yanzu Adams Oshiomhole ne shugaban jam'iyyar APC na kasa," in ji Ebegbulem a wata sanarwa da ya aike wa BBC.
Tun farko dai Mai Shari'a Danlami Senchi ne na wata kotu a Abuja ya yanke hukuncin bayan karar da aka shigar cewa tuni aka dakatar da Mista Oshiomhole daga jam'iyyar APC a jiharsa ta Edo.
Wani mai suna Oluwale Afolabi ne ya shigar da karar.
Mista Afolabi ya fada wa kotun cewa tun da reshen APC na jihar...
Gwamna Babagana Zulum ya bayyana cewa kiris ya rage da ya barke da kuka, a lokacin da ya ke raba kayan agajin jinkai da dimbin masu gudun hijira.
Zulum ya bayyana haka ne bayan aikin raba kayan abinci da sauran na masarufi ga masu gudun hijira da suka fito daga gidaje 19,000, a Gajiram, babbar hedikwatar Karamar Hukumar Nganzai ta Jihar Barno.
Gwamnan wanda shi da kan sa ne ya jagoranci dubagari da aikin sa-ido wajen raba kayan, ya ce ran sa ya baci matuka ganin irin halin kuncin rayuwar da Boko Haram suka jefa wadanda suka rasa muhallan su.
Sai ya ce, “shin har sai yaushe mutanen mu za su daina layin karbar abinci ne wai?
“Bai yiwuwa mu ci gaba da irin wannan rayuwar, wato rayuwar ci gaba da raba kayan abinci ga al’umma sun a shiga layi ...
Cutar coronavirus mai saurin yaduwa, na barazana ga hanyoyin samun kudin shiga na Najeriya.
a sakamakon haka , mai yiwuwa Gwamnatin Tarayya za ta sake duba kasafin kudinta na kimanin naira tiriliyan N10.59 wanda Majalisar Wakilai ta kasa ta gabatar a ranar 5 ga Disamba kuma shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan doka a ranar 17 ga Disamba, 2019.
Ministar kudi, da kasafi da tsare-tsare na kasa, Zainab Ahmed ita ce ta bayyana hakan yayin da ta ke yiwa manema labarai karin haske ga wakilan majalisar a karshen taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), wanda Shugaba Buhari ya jagoranta.
A cewarta, farashin mai na duniya ya ragu zuwa $ 52, a kasafin kudin da $ 57 kowace ganga.
Ministan, ta bayyana cewa arzikin man da kasar ke hakowa ya haura tsakani...
A Najeriya 'yan sanda sun kwace iko da hedikwatar jam'iyya mai mulki ta APC, inda suka girke jami'ansu da dama da kuma motocin domin hana shiga ofishin.
Matakin na zuwa ne sa'oi kalilan bayan wani hukuncin kotu da ya dakatar da shugaban jam'iyyar Adams Oshiomole.
Yan sanda sun fada wa BBC cewa an basu umarnin su hana kowa shiga komai mukaminsa.
Tsare ofishin baya rasa nasaba da rikicin shugabanci da jam'iyyar ta APC mai mulki ke fama dashi.
Kotu ta dakatar da Adams Oshiomole, bayan karar da wani dan jam'iyyar ya kai cewa tun a bara ne wata kotu ta dakatar da shugaban jam'iyyar, saboda haka babu dalilin da zai sa ya cigaba da jan ragaramar shugabanchin jam'iyyar.
Wannan ba shine karon farko ba da ak...
Kungiyar dadtawan kabilar Igbo, dake Kudancin Najeriya Ohanaeze Ndigbo, tayi gargadin cewa Ndigbo bazata hade hannu ta bar Fulani makiyaya su ci gaba da musgunawa al'ummarsu ba, ta hanyar fyade da kashe mutanen yan kinsu.
Shugaban Kungiyar Ohanaeze, Cif Nnia Nwodo, a wata budaddiyar wasika da ya aike wa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, mai taken,“ Hanyar fitina, ”a ranar Talata, ya ce Igbo a shirye suke dasu kare kansu daga duk wata fitina.
Nwodo, a wasikar sa ya bada labarin yadda yaran Fulani biyu suka fito da bindigogin AK-47 a fili cikin jama’ar Anambra inda kuma ya zargi Kwamishinan ‘yan sandan jihar da kin kama wadannan yaran,“ saboda sun fito daga wani yanki na kasar nan. ” a cewarsa.
Ya kuma tambayi Sufeto-janar na ‘yan sanda,“ Shin har yanzu ba a ba da izinin haramta...
Majalisar dokokin jihar Kano a arewacin Najeriya ta kafa kwamiti domin bincike kan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan wasu korafe-karafe biyu da aka gabatar mata.
Majalisar ta kafa kwamitin ne ranar Laraba karkashin dan majalisa Zubairu Hamza Masu, wanda shi ne shugaban kwamitin sannan an bai wa kwamitin mako daya ya gabatar da rahotonsa.
A yayin zaman majalisar na ranar Larabar ne shugaban kwamitin ya shaida wa majalisa cewa ya karbi korafi biyu daga wata Kungiyar Bunkasa Ilimi da Al'ada ta Kano da kuma wani Muhammad Mukhtar mazaunin unguwar Ja'en a karamar hukumar Gwale a ranar Litinin.
Ya ce masu korafin sun yi zargin cewa sarkin Kano ya yi wasu abubuwa da suka saba mutuntaka da addini da al'adar mutanen Kano.
Zubairu Masu ya ce masu korafin sun gabatar da faya-fayen CD a m...