
Bayan Kwashe kusan watanni 6 tana karyatawa a karshe dai, Hukumar Sojojin Saman Najariya ta amince da kuskuren harba bamabaman da suka kashe farar hula 39 a jihar Nasarawa
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Right Watch ta bayyana cewa, hukumar sojojin Saman Najariya ta amince da aikata kuskuren jefa bam a kauyen Kwatiri na jihar Nasarawa da ya kashe mutane farar hula 39.
A watan Janairu na shekarar 2023 ne dai aka samu wannan kuskure.
Dama dai a baya, Gwamna Abdullahi Sule na jihar ya bayyana cewa, ba sojojin saman Najariya ne suka aikata harin ba inda yace a ranar jirgin saman sojojin Najariya bai yi shawagi a yankin da lamarin ya faru ba.
Ya bayyana cewa, harin wani jirgi mara matuki ne da ba'a san wanene ke dashi ba ya kaishi.
Hukumar HRW tace tsaiko wajan amincewa da kai harin da sojojin Najariya suka yi bai taimakawa lamarin ba.
Tace kuma hukumar sojojin ta baiwa wadanda lamarin ya shafa diyya.