Saturday, June 6
Shadow

Tsaro

Gwamnatin Tarayya Ta Tura Dakarun Sojoji Zuwa Katsina Domin Kawo Karshen ‘Yan Bindiga

Gwamnatin Tarayya Ta Tura Dakarun Sojoji Zuwa Katsina Domin Kawo Karshen ‘Yan Bindiga

Tsaro
A yau Asabar 16 ga watan Mayun 2020, gwamnatin tarayya ta tura dakarunta don yaki da 'yan ta'addan da suka gallabi jihar Katsina, kamar yadda TheNation ta ruwaito.     Gwamna Aminu Bello Masari ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da aka yi da shi a wani gidan rediyo a Katsina. Masari ya ce dakarun sojin daga jihar da gwamnatin tarayya za a tura su sassan jihar ne don yaki da ta'addanci.     A yayin tattaunawa da gwamnan, ya jaddada cewa duk kalubalen tsaron ana kan shawo kansu, amma gwamnatin tarayya ce ke bada umarnin komai don ita ce mai rundunar sojin.     Ya kara da cewa, gwamnatin tarayyar ta samar da makamai da dukkan kayan aikin da sojin ke bukata don yaki da 'yan ta'addan.     Bincike ya nuna cewa, ka...
Yanzu-Yanzu:Katsinawa daga Yankin Jibia na zanga-zangar harin ‘yan Bindiga

Yanzu-Yanzu:Katsinawa daga Yankin Jibia na zanga-zangar harin ‘yan Bindiga

Tsaro
Wasu mutane daga kauyen 'Yangayya a jihar Katsina sun fito tsakiyar Titi wanda ya hada Garin Katsina da Jibia suka tare hanya inda sukace ba zasu bude ba sai gwamnati ta musu maganin harin 'yan ta'adda da suka addabesu. Masu zanga-zangar sun sa matafiya da dama tsayawa saboda babu hanyar wucewa. Sahara Reporters ta ruwaito cewa, kauyawan sun zargi Maharan da musu Fyade da Satar mutane dan kudin fansa.
Dakarun sojin Najeriya sun Kashe Mayakan Boko Haram da dama tare da lalata maboyarsu

Dakarun sojin Najeriya sun Kashe Mayakan Boko Haram da dama tare da lalata maboyarsu

Tsaro
Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa sojojin Sama sun yi Lugude akan maboyar mayakan kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa dake jihar Borno.   Me magana da yawun hedikwatar tsaron, Janar, John Enenche ne ya fitar da sanarwar.   Yace sun samu bayanan sirri cewa Mayakan sun karo yawa da kayan aiki inda suke shirye-shiryen kaiwa sojoji da sauran al'umma da basu ji basu gani ba hari.   Hakan yasa Rundunar sojin ta tashi jirgin yaki, a jiya, Juma'a kuma da yaje wajan ya ga mayakan kungiyar na hada-hada sosai.   Ya musu ruwan bama-bamai wanda ya kashe da dama, kuma aka lalata maboyar tasu.
Sojojin Najeriya sun kaiwa jihar Katsina dauki inda suka kashe ‘yan bindiga 27

Sojojin Najeriya sun kaiwa jihar Katsina dauki inda suka kashe ‘yan bindiga 27

Tsaro
Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta kai hari ta sama a garin Nahuta-Doumborou dake iyakar jihohin Zamfara da Katsina.   Harin yayi sanadin kashe 'yan bindiga 27 kamar yanda hedikwatar tsaro ta bayyana ta bakin me magana da yawunta,  Janar John Enenche.   Ya bayyana cewa an kai harinne bayan samun bayanan sirri kan cewa 'yan Bindigar na wajan inda yace sai jirgi ya kai musu hari ta sama.   Yace da dama sun mutu inda wasu suka gudu da raunuka, yace akwai shanun da 'yan Bindigar suka sato daga hannun mutane a wajan.   Ya kara da cewa daga baya sun samu bayanan sirri dake cewa 'yan Bindigar 27 ne suka bakunci lahira.   Ya godewa jama'a bisa hadin kan da suke baiwa sojoji wajan bayar da bayanan sirri inda yace su ci gaba da bayar
Rikicin ƙabilanci ya ɓarke a jihar Adamawa

Rikicin ƙabilanci ya ɓarke a jihar Adamawa

Tsaro
Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da ɓarkewar rikicin ƙabilanci a wani kauye na jihar.     Rikicin ya barke ne tsakanin Hausawa mazauna garin Tinno da kabilar Chobo da ke karamar hukumar Lamorde.     Ana fargabar cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a cikin rikicin.     Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa wani karamin saɓani aka samu bayan wani matashi ya kaɗe wani ɗan ƙabilar Chobo.   Daga bisani `yan uwansa suka far ma mai babur ɗin, inda shi ma wasu suka yi kokarin kare shi, kuma wasa-wasa rikici ya girma.     Wani mazaunin garin, Sulaiman Bello mazaunin, ya shaida wa "Muna cikin mawuyacin hali saboda yanzu an yi mana ƙawanya ko ta ina kana jin ƙ
Yanzu-Yanzu: Yanzu Haka ‘yan Bindiga na can suna kaddamar da hari a garin ‘Yankara na jihar Katsina

Yanzu-Yanzu: Yanzu Haka ‘yan Bindiga na can suna kaddamar da hari a garin ‘Yankara na jihar Katsina

Tsaro
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un   Labarin da muke samu da dumi-dumi shine yanzu haka 'yan bindiga na can garin 'yan kara nanjihar Katsina suna kaddamar da hari akan garin.   Rahoton yace 'yan bindigar na harbe-harbe kuma suna tatara Shanu, kamar yanda wata Majiya ta gayawa Sahara Reporters.   A 'yan kwanakinnan dai ana samun yawan hare-haren a jihar ta katsinsar wanda ke sanadin salwantar rayuka da dukiyoyin Al'umma.
Kalli Bidiyon Yanda sojoji suka kashe dan Boko Haram a Dajin Borno yayin da yake shirin guduwa

Kalli Bidiyon Yanda sojoji suka kashe dan Boko Haram a Dajin Borno yayin da yake shirin guduwa

Tsaro
Wani faifan bidiyo daya bayyana Shafukan sada zumunta ya nuna yanda wani mayakin Boko Haram ya bakunci Lahira bayan Gamuwa da sojoji wanda daga yanayin maganar da suke ga dukkan alamu daga kasar Nijar suka fito.   Bidiyon ya nuna Sojojin a cikin wata motar yaki suna tafiya, kwatsam sai ga dan Boko Haram din yana shirin tserewa.   Sun yi kokarin kiransa da ya tsaya amma yaki tsayawa, dan hakane suka harbeshi sannan motar tasu ta yaki tabi ta kanshi.   Shafin HumAngle da ya kware wajan kawo labarai kan matsalar tsaro a yankin Borno ne ya wallafa Bidiyon.   Bidiyon dai bai nuna yanda aka kashe dan Boko Haram din ba har karshe saboda an dusasheshi amma dai anji sojojin na fadar cewa ya mutu, wasu kuma na cewa be mutu ba. https://twitter.co...
Zakaran da Allah ya nufa da Chara: Jaririyar da aka harba sau 2 a harin da ISIS suka kai dakin Haihuwa a Kabul ta rayu

Zakaran da Allah ya nufa da Chara: Jaririyar da aka harba sau 2 a harin da ISIS suka kai dakin Haihuwa a Kabul ta rayu

Tsaro
A ranar Talatar data gabatane mayakan kungiyar dake ikirarin jihadi ta ISIS suka kai hari babban birnin kasar Afganistan, Kabul inda ta kashe akalla mutane 24.   Akwai jaririya wadda awanni 3 kacal da haihuwarta wadda aka harba har sau 2 a kafa yayin harin. Maharan sun shiga Asibitin, bangaren haihuwa su 3 sanye da kayan jami'an tsaro, suna shiga suka watsa ababen fashewa, aka fara batakashi dasu da jami'an tsaro. Daga karshe dai an samu kashesu saidai sunyi sanadin kashe mutane 24 ciki hadda jarirai sabuwar haihuwa 2 da mata da maza.   Mahaifiyar jaririya, Nazia da aka harba sau 2 a kafa ta rasu a sadain harin kuma tuni Likitoci suka mata aiki a kafar da aka harbeta. Mahaifin jaririyar, Rafiullah ne ya sakawa diyar rashi sunan Nazia wanda shine suna...
Makamai Sun Fada Gidajen Jama’a Sakamakon Fafatawa Da Boko Haram A Maiduguri

Makamai Sun Fada Gidajen Jama’a Sakamakon Fafatawa Da Boko Haram A Maiduguri

Tsaro
Sakamakon wata arangama tsakanin jami'an sojin Najeriya da wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne, wasu makamai sun fada kan wasu gidaje biyu a anguwar Bintu Suga dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.     Jami’an sojin Najeriya sun ce sun samu nasarar kashe wasu 'yan Boko Haram su 9, tare da kwace makamai 2.   Wani mazunin unguwar Binta Suga Muhammad Musa wanda lamarin ya shafa, ya shaidawa wakilin muryar Amurka cewa yana zaune a kofar gidansa da misalin karfe shida da kusan minti talatin, yaga wata wuta daga sama ta taso ta fada cikin gidan sa, amma babu wanda ya mutu ko ya sami wani rauni. Sannan ya ce jami’an ‘yan Sanda da Soji duka sun zo sun duba yanayin.   Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya Kanal Sagir Musa ya