fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tsaro

Mayakan ISWAP sun hallaka jami’an tsaro da farar-hula a Borno

Mayakan ISWAP sun hallaka jami’an tsaro da farar-hula a Borno

Tsaro
Mayakan jihadi sun kai hari sansanin soji da wani yankin Borno tare da kashe sojoji 9, da 'yan sanda biyu da kuma farar-hula, kamar yada majiyoyin tsaro da mazauna yanki suka tabbatar. Mayakan IS sun farwa garin Malam Fatori, a ranakun daren Juma'a da kuma safiyar Asabar, a cewar majiyoyin. A cewar bayanan da aka fitar, an tafka asara sosai a harin. Harin na farko, a kusa da iyakar Najeriya da Nijar anyi ɓarin wuta sosai tsakanin sojoji da mayakan, a cewar Buji Garwa. A watan Maris da ya gabata ne, dubban mutane da rikicin Boko Haram ya tilastawa tserewa zuwa Nijar, suka dawo yankunansu a Malam Fatori.
Sojoji sun sanar da kashe kasurguman ‘yan bindiga a Kaduna da Zamfara

Sojoji sun sanar da kashe kasurguman ‘yan bindiga a Kaduna da Zamfara

Tsaro
Rahotanni daga Najeriya na cewa sojoji sun kashe 'yan bindiga da dama a hare-haren sama da suka kaddamar kan maɓoyarsu a jihohin Kaduna da Zamafara. Jaridar Daily Trust a Najeriya ta rawaito cewa a Kaduna, sojojin sun kai harin ne kan wani shugaban 'yan bindiga Alhaji Gana a karamar hukumar Kinandan, da Ali Kawaje da Musa Pajelo da Kachalla Bello a Birnin Gwari. An kuma tarwatsa 'yan bindiga kuma a yankin Walawa da Fadaman Kanauta da Kuduru, kamar yada jaridar ta ambato Samuel Aruwan na cewa. A Zamfara kuma jiragen sojin Najeriya sun yi luguden wuta a yankin Shinkafi. Kakakin sojojin Najeriya Edward Gabkwet ya ce jami'ansu na cigaba da daukar matakai fatatakar 'yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya. Hare-haren saman na zuwa ne kwanaki bayan 'yan bindiga sun kashe mutum 44 a Zamf...
An kama Fastuwa dake baiwa masu garkuwa da mutane bayanan membobin cocinta suna sacesu a jihar Adamawa

An kama Fastuwa dake baiwa masu garkuwa da mutane bayanan membobin cocinta suna sacesu a jihar Adamawa

Tsaro
Jami'an tsaro na 'yansanda a jihar Adamawa sun kama wata Fastuwa mace me suna Ruth Kenneth dake da shekaru 37 bisa baiwa masu garkuwa da mutane bayanan membobin cocinta.   Matar na da yara 7 kuma mutane na zuwa wajanta neman magani.   An kamata ne bayan samunta da hannu dumu-dumu a barazanar garkuwa da daya daga cikin wanda take baiwa magani idan bai bayar da Naira Miliyan 10 ba.   Jami'an tsaron sun baiwa mutane shawarar su kiyaye yanda suke gudanar da ayyukansu da kuma kaiwa membobinsu bayanai kan abubuwan da basu gane ba.
Yan sandan Kebbi sun ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su

Yan sandan Kebbi sun ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su

Tsaro
Rundunar 'yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su a garuruwan Bena-Mairairai da Ruwan Kanwa na jihar. Kwamashinan 'Yan Sanda Ahmed Magaji Kwantagora ya bayyana yayin taron manema labarai a Birnin-Kebbi cewa 'yan fashin sun tare hanyar shiga Bena-Mairairai, inda dakarunsa suka yi wa wajen tsinke bayan samun rahoton hakan. Bayan fafatawa tsakanin ɓangarorin ne kuma aka yi nasarar ceto Jamila Ahamad, da Shamsiya Ahamad, da kuma Tasi’u Haruna. A wani lamarin daban kuma, kwamashinan ya ce dakarun sun ceto wasu mutum huɗu a yankin Jega da ke jihar waɗanda su ma 'yan bindiga suka yi garkuwa da su. Yayin samamen, 'yan sanda sun ƙwace mota ƙirar Toyota Corolla daga hannun 'yan fashin, "sannan an tsaurara sintiri don hana mahara sakat a yankin," in ji shi....
Jirgin yaƙin sojin Najeriya ya kai hari kan maɓoyar ‘yan bindiga

Jirgin yaƙin sojin Najeriya ya kai hari kan maɓoyar ‘yan bindiga

Tsaro
Rundunar Sojin sama ta Najeriya ta ce jirgin yaƙinta ƙarƙashin rundunar Operation Hadarin Daji ya ƙaddamar da hare-hare ranar 18 ga watan Nuwamba kan maɓoyar wani fitaccen shugaban 'yan bindiga mai suna Mallam Ila a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin saman Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar ranar Lahadi ya ce an kai hare-haren ne kilomita tara daga gabashin ƙauyen Manawa a ƙaramar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara. Sanarwar ta kuma tabbatar da kashe 'yan fashin daji bakwai, yayin da shi Mallam Ila ya kuɓuta bayan ya samu munanan raunuka. Mallam Ila na ɗaya daga cikin mutanen da rundunar ke nema saboda kusancinsa da fitattun shugabannin 'yan ta'adda kamar su Bello Turji da Dan Bokoyo. 'Yan ta'addan da ke ƙarƙashin dab...
An harbe mutum biyar a gidan casu na ƴan Luwadi a Amurka

An harbe mutum biyar a gidan casu na ƴan Luwadi a Amurka

labaran duniya na yau, Tsaro
An harbe mutum biyar a gidan casu na ƴan neman-maza a Amurka Mutum aƙalla biyar ne suka mutu sannan wasu 18 suka jikkata lokacin da wani mutum ya buɗe wuta a wani gidan rawa na 'yan luwaɗi da ke Colorado ta Amurka, in ji 'yan sanda. "Cikin baƙin ciki nake sanar da ku cewa an yi harbe-harbe a wani gidan casun dare a daren nan," in ji kakakin 'yan sanda Pamela Castro. BBC ta rawaito cewa Castro ya ce dakaru sun kai ɗauki "kuma mun ga wani da muke zargi shi ne maharin a cikin kulob ɗin da ake kira Club Q". Club Q ya fitar da sanarwa cewa "mun kaɗu da irin wannan hari na rashin hankali a kan mutanenmu".
Yansandan Katsina sun cafke wata da ta jefa dan kishiyarta rijiya ya mutu

Yansandan Katsina sun cafke wata da ta jefa dan kishiyarta rijiya ya mutu

Tsaro
Yansandan Katsina sun cafke wata da ta jefa dan kishiyarta rijiya ya mutu. Rundunar Yansandan jihar Katsina tayi nasarar cafke wata mata mai shekaru sha 18 da ake zargin ta da kashe dan kishiyarta ta hanyar jefata rijiya. Matar mai suna Maryam Habibu dake zaune a kauyen Leko na karamar hukumar Danja ta jefa dan kishiyarta dan shekaru 4 a duniya rijiya biyo bayan sakinta da Baban yaron yayi Allah shi kyauta Data Shafin Tabarau Gazette.
‘Yan sandan Jihar Neja sun ‘kashe ƴan fashin daji’ bakwai

‘Yan sandan Jihar Neja sun ‘kashe ƴan fashin daji’ bakwai

Tsaro
Mazauna Kumbashi na Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja a arewacin Najeriya sun samu sauƙi a hare-haren 'yan fashin daji sakamakon kashe wasu daga cikin maharan da 'yan sandan jihar suka yi a ranar Alhamis. Kafar talabijin ta Channels TV ta ruwaito kakakin 'yan sandan Neja, Wasiu Abiodun, fafatawar da jami'ansu suka yi tare da haɗin gwiwar mayaƙan sa-kai ta haddasa mutuwar 'yan fashi bakwai. Mista Abiodun ya ce mazauna yankin ne suka kai musu rahoto bayan sun ga gilmawar 'yan bindigar, inda su kuma suka far musu tare da fatattakar wasu ɗauke da raunuka. Sai dai ya ce mutum biyu daga cikin mayaƙan sa-kan sun ji raunuka kuma an kai su Babban Asibitin Kontagora don ba su kulawa.