fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tsaro

An kama ‘yansandan boge 5 a jihar Nasarawa

An kama ‘yansandan boge 5 a jihar Nasarawa

Tsaro
'Yansanda a jihar Nasarawa sun bayyana cewa, sun kama 'yan fashi biyar dake karya da cewa su 'yansanda ne.   Kakakin 'yansandan jihar, Rahman Nansel, ne ya bayyana haka inda yace an kama wadanda ake zargin akan hanyar Keffi zuwa Abuja.   Wadanda aka kama sune Aminu Adamu, Adamu Mohammed, Rilwanu Bala, Kabiru Usman, da Bashir A. Bashir.   Yace kwamishinan 'yansandan jihar ya bayar da umarnin yin binciken kwakwaf akan lamarin.
An kama matar data sace diyar makwabtanta

An kama matar data sace diyar makwabtanta

Tsaro
Jami'an tsaro sun kama wata mata data sace diyar makwabtanta.   An kama Miss Chinwendu Umegbaka me kimanin shekaru 38 ne da yarinyar me shekaru 3 da niyyar sayar da ita. Kakakin 'yansandan jihar Anambra inda lamarin ya faru ya bayyana cewa, bayan kama matar, an mayarwa da iyayen yarinyar diyarsu.   Yace suna ci gaba da bincike kan lamarin.
Hukumar NDLEA ta kama mutumin da ya hadiyi kullin koken 90 a Lagos

Hukumar NDLEA ta kama mutumin da ya hadiyi kullin koken 90 a Lagos

Tsaro
Hukumar yaki da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi ta Najeriya ta ce ta kama hodar Iblis ta hiroin da nauyinta ya kai kilogram 23.55, wadda aka boye a cikin katan-katan na abincin jarirai. Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, wanda ya bayyana labarin ya ce an kama hodar Iblis din ne, wadda kudinta ya kai sama da naira biliyan 4.5, kwatankwacin dala miliyan 10.8, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos, bayan an shigo da ita kasar ta wani jirgin sama na Afirka ta Kudu daga birnin Johannesburg. Jami'an hukumar sun ce an damke mutum uku da ake zargi da lamarin, wadanda suka hada da wasu ma'aikatan kamfanin dakon kaya da ainahin wanda zai karbi kayan, mai suna Chike Ikeke Eweni. Haka kuma hukumar ta NDLEA, ta ce ta kama wani bireba, Muyiwa Babalola Bolujoko, wanda ya hadiyi...
An damke ma’aikatan banki da suka hada kai ‘yan damfara don satar naira biliyan 3.4

An damke ma’aikatan banki da suka hada kai ‘yan damfara don satar naira biliyan 3.4

Tsaro
Inspecta janar na 'yan sanda Usman Baba ya jinjinawa hukumar saboda namijin kokarin da take yi a kwanakin nan. Kuma yace ba zasu laminci irin wa'yan nan lafukan da miyagun mutane ke aikatawa ba, sannan barayi ba zasu taba samun walawala ba a Najeriya. Shugaban 'yan sandan ya bayyana hakan ne bayan hukumar ta damke wasu ma'aikatan Banki da suka hada kai 'yan damfar don satar naira Biliyan 3.4. Inda yace yana jinjinawa hukumar 'yan sanda na jihar Oyo da suka dakatar da wannan iftila'in.
PDP ta bukaci gwamnatin shugana Buhari ta gudanar da bincike akan tsohon shugaban soji, janar Burtai kan satar kudin makamai daya yi

PDP ta bukaci gwamnatin shugana Buhari ta gudanar da bincike akan tsohon shugaban soji, janar Burtai kan satar kudin makamai daya yi

Tsaro
Jam'iyyar PDP ta bukaci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari data gudanar da bincike akan shugaban sojoji, janar Burtai. PDP ta bayyana haken ne bayan da hukumar ICPC ta kwace kudade a hannunsa har naira biliyan 1.85 wanda ake sa ran na makamai ne ya sata. Kuma hadda motocin alfarma duk a gidan nasa da kuma gidan wani mutun wanda duk yace na Burtai ne kayayyakin miliyoyin kudin da aka gani a hannunsa. Kuma ana kyautata kudaden da Buhari ya bayar ne don a sayi bindugu a yaki Boko Haram dasu.
Kasar Amurka na kokawa saboda matasanta basa son shiga aikin soja

Kasar Amurka na kokawa saboda matasanta basa son shiga aikin soja

Tsaro
Kasar Amurka tace 'yan kasarta matasa kadanne suka cancanci shiga aikin soja kuma a cikin kadandin, da yawa basa son aikin.   Sanarwar tace yawanci abinda ke hana matasan shiga aikin sojan shine tsoron samun rauni, mutuwa da tabuwar kwakwalwa.   Hukumar sojojin ta koka da wannan lamari inda tace yana ci mata tuwo a kwarya, karin abinda ke sa ana samun karancin masu shiga aikin sojan a kasar Amurka shine dokokin dake tattare da daukar aikin.
Kalli fuskokin wasu masu garkuwa da mutane da aka kama

Kalli fuskokin wasu masu garkuwa da mutane da aka kama

Tsaro
Wadannan wasu masu garkuwa da mutanene da aka kama a jihar Ekiti.   Wadanda aka kama din sune  Abashe Adamu Idris, da Ibrahim Mumini Toyin. Kakakin yansandan jihar, DSP Sunday Abutu ya bayyana cewa wanda aka kama din sune ake zargin na da hannu a garkuwa da mutane da yawa a jihar.   Yace bayan lokaci me tsawo sun yi nasarar kama wanda ake zargin kuma idan suka kammala bincike zasu gurfanar dasu a gaban kuliya.
Yadda sojoji suka babbake min mahaifina tare da gidanmu a jihar Patakwal, cewar wata mata

Yadda sojoji suka babbake min mahaifina tare da gidanmu a jihar Patakwal, cewar wata mata

Tsaro
Yaran wani mutun dn shekara 70 Cletus Ofem, Esther da Aaliyah sun bayyana cewa sojoji sun babbake mahaifinsu tare da gidansu baki daya. Yaran sun bayyana cewa al'ummar karamar hukumar Yukurr dake jihar Patakwal ne sukayi fada da sojojin har suka kashe daya daga cikinsu. Saboda haka ne sojojin suka dawo daukar fansa wanda anan ne suka babbake masu mahaifin nasu. Inda yaran suka kara da cewa mahaifin nasu ba zai iya tserewa ba yayin da sojojin sukaje gidan domin bashi da lafiya sosai, kuma sojojin sun san cewa mahaifin nasu yana cikin gidan.