
Hukumar Soji ta kama sojannan da ya caccaki Buratai da Buhari kan kashe-kashen Arewa
Hukumar soji ta kama soja, Lance Corporal Martins da muka kawo muku labarin shi jiya cewa ya caccaki gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan rashin tsaro.
Sojan a wani Bidiyo da Sahara Reporters ta wallafa ya bayyana cewa, an jishi yana cewa Shugaban sojojin,Janar Tukur Yusuf Buratai, Me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Majo Janar Babagana Mungono, Murabus da shugaban hedikwatar tsaro janar Gabriel sun ji kunya.
Yace duk da yake cewa manyan sojojin Kasarnan da shuwagabannin tsaro 'yan Arewane amma sun bari ana ta kashe mutane a Arewar. Yace dan haka ya yanke shawarar kai su kotun Duniya kuma yana neman lauyiyin Najeriya su goya mai baya.
Sabon Rahoton da Sahara Reporters ta wallafa na cewa wannan sojan tuni aka kamashi bisa umarnin shug...