fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Tsaro

Yan bindiga sun kai hari kan ƙauyukan Katsina, inda suka kashe mutum 3

Yan bindiga sun kai hari kan ƙauyukan Katsina, inda suka kashe mutum 3

Tsaro
'Yan bindiga a daren ranar Alhamis sun kai hari kan kauyukan Madobai da Dannakwabo na karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu da yawa.  Mazauna garin sun ce da yawa daga cikin dabbobinsu da kayan abinci su 'yan fashi suka kwashe bayan mamayar.   A Cesar wata majiya mazauna yankin sun binne gawarwakin da safiya bayan sun musu sallar jana'iza haka zalika majiyar ta bayyana yadda mazauna yankin suka koka bisa yawan harin da ake kaiwa yankin nasu. Hakan ya zo ne kwana guda bayan da aka kai hari kauyen Mabai a cikin gunduma guda daya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wani manomi, Sada Musa, yayin da wani Karibu Mohamed aka harba da harsashi.     Mazauna kauyen sun yi ƙoƙari su tare harin amma a sakamakon yawan da 'yan bindigar ke dashi wanda ...
Bidiyo:Kalli yanda Jirgin saman Sojin Najeriya yawa maboyar Boko Haram Fatafata, Da yawan mabiya kungiyar sun mutu

Bidiyo:Kalli yanda Jirgin saman Sojin Najeriya yawa maboyar Boko Haram Fatafata, Da yawan mabiya kungiyar sun mutu

Tsaro
Hadikwatar tsaro ta kasa ta bayyana cewa sojojin Saman Najeriya dake rundunar Operation Lafiya Dole sun kaiwa mayakan Boko Haram hari a garin Parisu dake jihar Borno.   Mayakan na Boko Haram da yawa sun halaka a harin inda kuma aka lalata kayansu da rusa musu gine-gine.   Hakan na zuwane bayan samun bayanan Sirri akan kungiyar dake cewa sun taru suna shirin kaiwa sojojin hari.   Kalli bidiyon yanda harin ya kasance. https://twitter.com/DefenceInfoNG/status/1256201170692931585?s=19 An yi bincike kuma an tabbatar da haka, kamar yanda sanarwar ta bayyana, daga nanne sai rundunar ta sojin sama ta aika jiragenta suka yi ruwan bama-bamai akan 'yan ta'addar.  
Yan sanda sun kama mutum 3 saboda cin mutuncin Shugaba Buhari, Masari a shafukan sada zumunta

Yan sanda sun kama mutum 3 saboda cin mutuncin Shugaba Buhari, Masari a shafukan sada zumunta

Tsaro
A ranar Alhamis din da ta gabata ne rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ta ce ta kama mutane uku a wani faifan bidiyo a kafafen sada zumunta da ake zargi da cin mutuncin Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar, Aminu Masari. Wadanda aka kama din sune; wani mutum dan shekara 70, Lawal Abdullahi Izala; Bahajaje Abu da Hamza Abubakar dukkansu na zaune a Gafai Quarters, a cikin garin Katsina. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce, an jawo hankalin rundunar‘ yan sanda ta jihar Katsina ne ta wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna wani Lawal Adullahi, wanda ake kira “IZALA” wanda ke zagin Shugaban Kasa Buhari da gwamna Masari. Saboda haka, Kwamishinan 'yan sanda, CP Sanusi Buba, ya ba da umarnin gudanar da bincike wanda hakan ya sany...
Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 11sun kwace makamai

Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 11sun kwace makamai

Tsaro
Sojojin Najeriya sun sake kashe wata bataliyar ‘yan ta’addan Boko Haram 11 a kokarin da rundunar take na kakkabe ayyukan 'yan kungiyar tada kayar baya dake a yankin Arewa Maso Gabas Hakan na  ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja a ranar Laraba ta Babban Jami'in Harkokin Watsa Labarai, Ma'aikatar Tsaro, Manjo Janar John Enenche, game da ayyukan rundunar sojojin Najeriya a 'yan kwanakin da suka gabata. Rundunar ta bayyana kwace makamai da bindiga kirar AK-47 tare da babur hadi da abubuwa masu fashewa. A dai 'yan kwanakin nan rundunar sojin Najeriya ta zafafa wajan kai farma ki ga masu tada kayar baya.
Majalisar dokokin Chadi ta soke hukuncin kisa kan ‘yan ta’adda

Majalisar dokokin Chadi ta soke hukuncin kisa kan ‘yan ta’adda

Tsaro
Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da wata doka da ta hana aiwatar da hukuncin kisa kan mutanen da aka samu da aikata laifuffukan da suka shafi ta’addanci.     Ministan shari’ar kasar Djimet Arabi ya sanar da dfaukar matakin, shekaru 4 bayan Chadi ta jingine aiwatar da hukuncin kisa kan kowanne laifi.     Arabi wanda ya gabatar wa majalisar dokoki da kudirin yace 'yan majalisun sun amince da dokar ba tare da hamayya ba.     Ministan yace matakin wani yunkuri ne na samar da dokar bai daya kamar yadda kasashen yankin Sahel suka yi, kuma dokar zata fara aiki da zarar shugaba Idris Deby ya rattaba hannu akan ta.
Ban yadda da cewa Shekau zai mika Wuya ba kuma ana Amfani da tsaffin hotuna dan nuna cewa Sojoji na nasara akan Boko Haram >>Audu Bulama Bukarti

Ban yadda da cewa Shekau zai mika Wuya ba kuma ana Amfani da tsaffin hotuna dan nuna cewa Sojoji na nasara akan Boko Haram >>Audu Bulama Bukarti

Tsaro
A ‘yan kwanakin nan ana ta rade-radin cewa jagoran Boko Haram, Abubakar Shekau yana so ya mika wuya ga mahukuntan Najeriya.     A lokacin da Babban jami’in cibiyar samar da bayanai a hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar John Enenche ke tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, ya ce “muddin Shekau ya bi tsarin da ake bi a kasar nan wajen mika wuya, toh, tabbas za mu karbe shi.”     Shi ma kakakin sojojin Najeriya, Kanar Sagir Musa ya tabbatar da jin wannan jita-jitar.     “Muna da labarin cewa Shekau yana so ya mika wuya, amma wannan ba shi ke gabanmu ba, yakin da muke yi shi ya dame mu,” a cewar kakakin.     Sai dai tun da aka fara yada wannan jita-jitar mutane suka fara saka alamar tambaya kan lamarin.  ...
Kotun tafi da gidan ka tafara hukunta masu karya doka a kano

Kotun tafi da gidan ka tafara hukunta masu karya doka a kano

Tsaro
An fara hukunta masu karya doka a kano Bayan sanya dokar hana zirga-zirga a jihar kano. Gwamnatin jihar ta kafa kotun tafi da gidan ka wadda ke hukunta masu kunnan kashi akan dokar da gwamnati ta sanya na hana zirga-zirga a sakamakon bullar cutar corona jihar. Tuni dai kotunan suka fara aiki a gurare daban daban a kwaryar birnin kano a ranar talata. Inda aka rawaito kotun dake zaune a gadan kaya  dake karamar hukumar gwale  ta samu wasu da laifin fita ba bisa ka'ida ba, inda kotun ta hukunta wani mai suna Sani Usman, wanda ya bayyana cewa "Naje ne in siyo Gas din abinci aka kamani. Injishi Kotun dai tai masa tarar Naira  dubu 2 Wanda nan take ya biya aka salla me shi.
Masu zanga zanga sunyi arangama da jami’an yan sanda inda suka jikkata jami’ai 5 a jihar legas

Masu zanga zanga sunyi arangama da jami’an yan sanda inda suka jikkata jami’ai 5 a jihar legas

Tsaro
Lamarin ya faru ne a jihar legas inda wasu ma’aikata a matatar man Dangote da kuma masu aiki a tashar shigar da kayayyaki daga kasashen waje sun yi arangama da jami’an ‘yan sanda lokacin da suka nemi rufe wuraren da suke aiki a unguwar Lekki.   Wasu da suka shaida aukuwar lamarin sun ce, fadan ya kaure ne a lokacin da wasu matasa suka cinnawa tayoyi wuta akan tituna, tare da zargin jami’an tsaro da fifita wani bangare yayin tilasta bin dokar hana fitar dake aiki a unguwar at Lekki, don dakile yaduwar annobar coronavirus.   Kakakin 'yan sandan jihar ta Legas Bala Elkana, yace masu zanga-zangar sun raunata jami’ansu guda 5, yayinda su kuma suka kama 51 daga cikin su.      
ISWAP/Boko Haram na shirin sake daukar sabbin mayaka>>MNJTF

ISWAP/Boko Haram na shirin sake daukar sabbin mayaka>>MNJTF

Tsaro
Rahotanni daga jihar Borno na cewa mayakan kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram na shirin fara daukar sabbain maayaka.   Labari ne aka samu na sirri daga majiya me kyau, kamar yanda tawagar gayammar kasashen yankin tafkin Chadi,MNJTF dsta hada kasashen Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru dake yai da ta'addanci ta bayyanar.   Me magana da yawun tawagar, Col. Timothy Antigha ya bayyana cewa, ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar a Maiduguri.   Yace ISWAP na kokarin ganin ta maye gurbin mayakanta data rasa ta hanyar satar matasa maza da kuma wa'azi na canja tunani akan Jahadi.   Dan haka tawagar take kira ga matasa a yankin su lura sannan iyaye suma su lura da kuma shuwagabannin al'umma da saka ido akan 'ya'yansu, kada a musu kwadaitarwar ...
Hoto:Dubu 6 muke karba daga hannun ‘yan Bindigar Zamfara kamin mu yadda su yi lalata damu>>Inji Wadannan ‘yan matan

Hoto:Dubu 6 muke karba daga hannun ‘yan Bindigar Zamfara kamin mu yadda su yi lalata damu>>Inji Wadannan ‘yan matan

Tsaro
Wasu 'yan mata 2, 'yan uwan juna da aka kama a jihar Zamfara tare da wani dan Achaba da ake zargi yana kaiwa 'yan bindigar jihar Zamfara kayan Masarufi da matan banza sun amsa cewa Dubu 6 suke karba daga gurin 'yan bindigar kamin su amince su yi lalata dasu.   Hukumar 'yansandan Civil Defence ta jihar Zamfarace ta kama Shafi'u Abdullahi da 'yan matan 'yan uwan juna, Binta Husaini da Balki. An kamasu ne akan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Anka inda acanne suke kaiwa 'yan Bindigar kayan masarufi.   Kwamandan Civil Defence din, Aliyu Garba yace Ranar Juma'ane aka kama mutanen akan hanyarsu bayan da dubunsu ta cika, bayan samun bayanan sirri da aka yi.   Ya kara da cewa, An kamasu ne akan hanyar Bagega zuwa Anka inda dan mashindin din zai kai 'yan matan 2 mas...