
Ku tashi tsaye wajan aiki haikan ko kuma a koreku>>Sanata Ahmad Lawal ga Shuwagabannin tsaro
Kakakin majalisar tarayya, Sanata Ahmad Lawal ya gargadi shuwagabannin tsaro da su tashi haikan wajan aiki dan shawo kan matsalar tsaro ko kuma a koresu daga aiki.
Lawal ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai bayan zantawa da shugaban kasa, a yau.
Yace zasu samar da kayan aiki da duk wani taimako daya kamata amma fa idan aka samu wani da baya bayar da sakamakon da ake so to za'a sallameshi.