
Ruwa yaci Mutane 6 ciki hadda me ciki yayin da suke kokarin tsallake ruwan dan gujewa harin ‘yan ta’adda a Batsari jihar Katsina
A daren Juma'a ne wasu 'yan Bindiga suka kai hari kauyukan Nahuta da Kasai dake karamar hukumar Batsari jihar Katsina inda suka kashe mutum 1 sannan wasu 2 sun bace.
Majiyoyi daga garin sun bayyana cewa mutane 6 ne ciki hadda me cike ruwa yaci a yayin da suke kokarin tserewa harin 'yan bindigar.
A ranar An yi ruwan sama sosai, mutane da dama sun shiga daji dan tsira da rayukansu yayin da 'yan bindigar suka rika harbin kan me uwa da wabi, kamar yanda Sahara Reporters ta ruwaito.
'Yan bindigar sun ci karensu ba babbaka har suka gama suka tafi babu jami'an tsaron da suka kaiwa mutanen garin dauki.
A daren jiya,Asabar ma an sami wani harin a kauyen Salihawar Dan Alhaji duk a karamar hukumar ta Batsari.